[1] Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce,
[2] “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.
[3] “Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.
[4] Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba.
[5] Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina,
[6] amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.
[7] Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.
[8] Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki.
[9] Kwana shida za ka yi dukan aikinka,
[10] amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.
[11] Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.
[12] Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.
[13] Ba za ka yi kisankai ba.
[14] Ba za ka yi zina ba.
[15] Ba za ka yi sata ba.
[16] Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.
[17] Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”
[18] Da mutane suka ga tsawa da walƙiya, suka ji karar ƙaho, suka kuma ga dutsen yana hayaƙi, sai suka yi rawar jiki don tsoro. Suka tsaya da nisa
[19] suka ce wa Musa, “Ka yi magana da mu da kanka, za mu kasa kunne. Amma kada Allah ya yi mana magana, don kada mu mutu.”
[20] Musa ya ce wa mutane, “Kada ku ji tsoro, gama Allah ya zo don yă gwada ku, don ku riƙa girmama shi, don kuma kada ku yi zunubi.”
[21] Sa’ad da mutane suka tsattsaya da nesa, sai Musa ya matsa kusa da girgije mai duhu, inda Allah yake.
[22] Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka faɗa wa Isra’ilawa wannan. ‘Kun gani da kanku cewa na yi magana da ku daga sama.
[23] Kada ku yi waɗansu alloli in ban da ni, kada ku yi wa kanku allolin azurfa ko na zinariya.
[24] “ ‘Ku yi mini bagaden ƙasa, ku kuma miƙa mini hadaya ta ƙonawa da hadaya ta salama, za ku hadayar da tumakinku da awakinku da shanu. Duk inda na sa a girmama sunana, zan zo wurinku, in sa muku albarka.
[25] In kuka yi mini bagade dutse, kada ku gina shi da sassaƙaƙƙun duwatsu, gama inda guduma ta taɓa duwatsun, sun haramtu ke nan.
[26] Kada ku gina wa bagadena matakala, domin kada yayinda wani yana hawa, mutane su ga tsiraicinsa.’