[1] Musa ya tara dukan jama’ar Isra’ilawa ya ce musu, “Waɗannan su ne abubuwan da Ubangiji ya umarce ku, ku yi.
[2] Kwana shida za ku yi aiki, amma rana ta bakwai za tă zama rana mai tsarki, Asabbaci ne na hutu ga Ubangiji. Duk wanda ya yi aiki a wannan rana dole a kashe shi.
[3] Kada ku hura wuta a cikin duk mazauninku a ranar Asabbaci.”
[4] Musa ya ce wa dukan jama’ar Isra’ilawa, “Ga abin da Ubangiji ya umarta.
[5] Daga cikin abin da kuke da shi, ku ɗauki kyauta domin Ubangiji, duk wanda yana niyya, sai yă kawo wa Ubangiji kyauta ta, “zinariya, azurfa da tagulla;
[6] shuɗi, shunayya da jan zare, lallausan lilin, da gashin akuya;
[7] fatun rago da aka rina ja, da fatun shanun teku; da itacen ƙirya
[8] da man zaitun don fitila; da kayan yaji don man shafewa, da kuma turare mai ƙanshi;
[9] duwatsun onis, da sauran duwatsu masu daraja waɗanda za a mammanne a efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
[10] “Duk waɗanda suke da fasaha a cikinku, su zo su yi dukan abin da Ubangiji ya umarta,
[11] “wato, aikin tabanakul da tentinsa tare da murfinsa, maɗauransa, katakansa, sandunansa da tussansa;
[12] akwatin alkawari da sandunansa, murfin kafara da labulen da ya rufe shi;
[13] tebur da sandunansa, da dukan kayansa da kuma burodin kasancewa;
[14] wurin ajiye fitila da yake don fitilu da kayayyakinsa, fitilu da mai don fitila;
[15] bagaden turare da sandunansa, man shafewa da turare mai ƙanshi; da labulen ƙofar shiga tabanakul;
[16] bagaden hadaya ta ƙonawa da rigarsa ta tagulla da sandunansa da duk kayayyakinsa, daron tagulla da wurin ajiye shi.
[17] Labulen filin tenti da sandunansa da tussansa, da kuma labulen ƙofar shiga fili;
[18] turakun tenti don tabanakul da kuma don filin, da igiyoyinsu;
[19] saƙaƙƙun riguna na sawa don hidima cikin wuri mai tsarki da tsarkakakkun riguna na Haruna firist, da riguna don ’ya’yansa maza lokacin da suke aiki a matsayin firistoci.”
[20] Sai dukan jama’ar Isra’ilawa suka janye daga fuskar Musa,
[21] duk waɗanda suke da niyya, waɗanda kuma zukatansu suka motsa su, suka kawo kyautai wa Ubangiji, don aikin Tentin Sujada, don duk aikinsa, da don tsarkakakkun riguna.
[22] Duk waɗanda suke da niyya, maza da mata, gaba ɗaya, suka kawo kayan ado na zinariya na kowane iri. ’Yan kunne, da ƙawane, da mundaye, da kayayyakin zinariya iri-iri. Dukansu suka miƙa zinariyarsu a matsayin hadaya ga Ubangiji.
[23] Kowane mutumin da yake da shuɗi, shunayya ko jan zare, ko lallausan lilin, ko gashin akuya, ko fatun rago da aka rina ja, ko fatun shanun teku, suka kawo.
[24] Masu miƙa kyautar azurfa, ko tagulla suka kawo su a matsayin kyautai ga Ubangiji, kuma kowane mutumin da yake da itacen ƙirya don kowane sashin aikin, ya kawo.
[25] Kowace mace mai fasaha ta kaɗa zare da hannuwanta, ta kuma kawo abin da ta kaɗa na shuɗi, shunayya, ko jan zare, ko lallausan lilin.
[26] Kuma dukan matan da suke da niyya, suke kuma da fasaha, suka kaɗa gashin akuya.
[27] Shugabannin suka kawo duwatsun Onis. Da duwatsu masu daraja don a jera a kan efod da ƙyallen maƙalawa a ƙirji.
[28] Suka kawo kayan yaji da man zaitun don fitila da don man shafewa da kuma don turare mai ƙanshi.
[29] Dukan mazan Isra’ilawa da matan da suke da niyya suka kawo wa Ubangiji kyautai na yardar rai, domin dukan aikin da Ubangiji ya umarce su ta bakin Musa.
[30] Sa’an nan ya ce wa Isra’ilawa, “Duba Ubangiji ya zaɓi Bezalel ɗan Uri, ɗan Hur, daga kabilar Yahuda,
[31] ya kuma cika shi da Ruhun Allah, da fasaha, azanci da kuma sani cikin dukan sana’ar hannu,
[32] don yă ƙirƙiro zāne-zāne na gwaninta waɗanda za yi da zinariya, da azurfa da kuma tagulla.
[33] Haka kuma wajen sassaƙar duwatsu na jerawa, da sassaƙar itace, da kowane irin aiki na gwaninta.
[34] Ya kuma ba Bezalel da Oholiyab ɗan Ahisamak, daga kabilar Dan, iyawa don koya wa waɗansu.
[35] Ya cika su da fasaha don yin kowane irin aikin sana’a, zāne-zāne, ɗinke-ɗinke shuɗi, shunayya da jan zare, da lallausan lilin, da kuma masu yin saƙa, sun gwaninta ƙwarai cikin kowane irin aikin hannu da kuma zāne-zāne.