[1] Yanzu ka duba fa, Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, yana shirin yă ɗauke kowane tanadi da taimako daga Urushalima da Yahuda dukan tanade-tanaden abinci da kuma dukan tanade-tanaden ruwa,
[2] jarumi, da soja, alƙali da annabi masu duba da dattijo,
[3] shugaban sojojin hamsin da mutum mai makami, mai ba da shawara, gwanin sarrafa abubuwa da mai gwanintan dabo.
[4] “Zan sa ’yan yara su zama shugabanninsu; ’yan yara kurum za su yi mulkinsu.”
[5] Mutane za su zalunci juna mutum da mutum, maƙwabci da maƙwabci. Yara za su rena tsofaffi, ƙasƙantacce zai rena mai daraja.
[6] Mutum zai kama ɗaya daga cikin ’yan’uwansa a gidan mahaifinsa ya ce, “Kana da abin sawa, ka zama shugabanmu; wannan kango kuma yă zama a ƙarƙashinka!”
[7] Amma a ranan nan zai tā da murya ya ce, “Ba ni ba dai. Ba ni da abinci ko abin sawa a gidana; kada ka mai da ni shugaban mutane.”
[8] Urushalima tana tangaɗi, Yahuda yana fāɗuwa; maganganunsu da ayyukansu suna gāba da Ubangiji, suna rena ɗaukakar kasancewarsa.
[9] Fuskokinsu shaidu ne a kansu; suna nuna zunubinsu a fili kamar yadda Sodom ya yi; ba sa ma ɓoye shi. Kaitonsu! Sun jawo wa kansu masifa.
[10] Ku faɗa wa masu adalci cewa kome zai zama musu da kyau, gama za su ji daɗin aikin da hannuwansu suka yi.
[11] Kaiton masu mugunta! Masifa tana a kansu! Za a rama abin da hannuwansu suka yi.
[12] Matasa suna zalunta mutanena, mata suna mulki a bisansu. Ya mutanena, jagorarinku suna ɓad da ku; suna karkatar da ku daga hanya.
[13] Ubangiji ya ɗauki mazauninsa a cikin ɗakin shari’a; ya tashi don yă shari’anta mutane.
[14] Ubangiji yana shari’a da dattawa da kuma shugabannin mutanensa, “Ku ne kuka lalace gonar inabina; ganimar talakawa suna a gidajenku.
[15] Ina dalilin da kuke marmatsa mutanena kuna gurgurje fuskokin talakawa?” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
[16] Ubangiji ya ce, “Matan Sihiyona suna da girman kai, suna tafiya da wuya a miƙe, da idanu masu yaudara, suna takawa ɗaya-ɗaya a hankali, da mundaye a ƙafafunsu, suna cas-cas.
[17] Saboda haka Ubangiji zai kawo gyambuna a kawunan matan Sihiyona; Ubangiji zai sa a aske kawunansu, a bar su ƙwal.”
[18] A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu,
[19] ’yan kunnensu, kwandagansu da lulluɓinsu,
[20] kitsonsu, sarƙar da suke sa wa damatsansu da ɗamararsu, kwalabai turare da layu,
[21] da ƙawanen da suka sa a yatsotsinsu da hancinsu,
[22] tufafi masu kyau, da manyan rigunansu, da mayafansu, da jakar kuɗinsu
[23] da madubi, da kuma tufafin lilin da adikai, da gyale.
[24] A maimakon ƙanshi, wari ne za a ji; a maimakon abin ɗamara, igiya ce za a samu; a maimakon kyakkyawan gashi, sanƙo za su kasance da shi a kai; a maimakon tufafi masu kyau, za su sa tsummoki; a maimakon kyau, za su zama munana.
[25] Mazanku za su mutu ta wurin takobi, jarumawanku za su mutu a yaƙi.
[26] Ƙofofin Sihiyona za su yi makoki su kuma yi kuka; za tă zama wofi, za tă zauna a ƙasa.