[1] Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai; zai sāke zaɓi Isra’ila yă kuma zaunar da su a ƙasarsu. Baƙi ma za su zo su zauna tare da su su haɗa kai da gidan Yaƙub.
[2] Al’ummai za su ɗauke su su kuma kawo wurin da yake nasu. Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummai a matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji. Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammu su kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.
[3] A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta,
[4] za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a. Mai danniya ya zo ga ƙarshe! Dubi yadda fushinsa ya ƙare!
[5] Ubangiji ya karye sandar mugaye, sandan mulkin masu mulki,
[6] wanda cikin fushi ya kashe mutane da bugu marar ƙarewa, kuma cikin fushi ya mamaye al’ummai da fushi ba ƙaƙƙautawa.
[7] Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama; sun ɓarke da waƙa.
[8] Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanon suna murna a kanka suna cewa, “Yanzu da aka ƙasƙantar da kai, babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.”
[9] Kabari a ƙarƙashi duk ya shirya don yă sadu da kai a zuwanka; yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka, dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya; ya sa suka tashi daga kujerun sarauta, dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai.
[10] Duk za su amsa, za su ce maka, “Ashe kai ma raunana ne, kamar mu; ka zama kamar mu.”
[11] An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari, tare da surutan garayunka; tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinka tsutsotsi kuma suka rufe ka.
[12] Yaya aka yi ka fāɗo daga sama Ya tauraron safiya, ɗan hasken asuba! An fyaɗa ka da ƙasa, kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!
[13] Ka yi tunani a ranka ka ce, “Zan hau zuwa sama; zan ɗaga kursiyina sama da taurarin Allah; zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro, a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.
[14] Zan haura can bisa gizagizai; zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.”
[15] Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari, zuwa zurfafan rami.
[16] Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido, suna tunani abin da zai same ka. “Wannan mutumin ne ya girgiza duniya ya kuma sa mulkoki suka razana,
[17] mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada, wanda ya tumɓuke biranenta bai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?”
[18] Dukan sarakunan duniya suna kwance a mace, kowa a kabarinsa.
[19] Amma an jefar da kabarinka kamar reshen da aka ƙi; an rufe ka da waɗanda aka kashe, tare da waɗanda aka soke da takobi, waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami. Kamar gawar da aka tattake da ƙafa,
[20] ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba, gama ka hallaka ƙasarka ka kuma kashe mutanenka. Ba za a ƙara ambaci zuriyarka masu aikata mugunta ba.
[21] A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa maza saboda zunuban kakanninsu; kada a reno su su gāji ƙasar su cika duniya da biranensu.
[22] “Zan yi gāba da su,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta, ’ya’yanta da zuriyarta,” in ji Ubangiji.
[23] “Zan mai da ita wuri domin mujiyoyi da kuma fadama; zan share ta da tsintsiyar hallaka,” Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.
[24] Ubangiji Maɗaukaki ya rantse, “Tabbatacce, kamar yadda na riga na shirya, haka zai kasance, kuma kamar yadda na nufa, haka zai zama.
[25] Zan ragargazar da Assuriya a cikin ƙasata; a kan duwatsuna zan tattake shi. Za a ɗauke nauyin da ya sa wa mutanena, a kuma ɗauke nauyinsa daga kafaɗunsu.”
[26] Wannan shi ne shirin da na yi domin dukan duniya; wannan shi ne hannun da aka miƙa a bisa dukan al’ummai ke nan.
[27] Gama Ubangiji Maɗaukaki ya ƙudura ya yi wannan, wa kuwa zai hana shi? Ya riga ya miƙa hannunsa, wa zai komar da shi?
[28] Wannan abin da Allah ya yi magana ya zo ne a shekarar da Sarki Ahaz ya mutu.
[29] Kada ku yi farin ciki, dukanku Filistiyawa, cewa sandar da ta buge ku ta karye; daga saiwar wannan maciji wani mugun maciji mai dafi zai taso, ’ya’yansa za su zama wani maciji masu dafi mai tashi sama.
[30] Mafi talauci na matalauta zai sami wurin kiwo, mabukata kuma za su kwana lafiya. Amma zan hallakar da saiwarka da matsananciyar yunwa; za tă kashe naka da suka rage da rai.
[31] Ki yi ihu, ya ke ƙofa! Yi kururuwa, ya ke birni! Ku razana, dukanku Filistiyawa! Ƙunshin hayaƙi yana tasowa daga arewa, kuma babu matsorata a cikin sojojinsa.
[32] Wace amsa ce za a bayar wa jakadun wannan al’umma? “Ubangiji ya kafa Sihiyona, kuma a cikinta mutanensa masu shan azaba za su sami mafaka.”