Listen to this chapter • 1:11
[1] A wannan rana za ku ce, “Zan yabe ka, ya Ubangiji. Ko da yake a dā ka yi fushi da ni, amma yanzu ka daina fushi da ni ka kuwa ta’azantar da ni.
[2] Tabbatacce Allah shi ne mai cetona; zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba. Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata; ya zama mai cetona.”
[3] Da farin ciki zan ɗebo ruwa daga rijiyoyin ceto.
[4] A wannan rana za ku ce, “Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa; a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai, a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.
[5] Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa; bari a sanar da wannan ga dukan duniya.
[6] Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona, gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”
Ishaya — Chapters
16:1223:3534:0841:2256:2362:4875:0584:2394:38106:29113:28121:11133:57145:55152:02163:19173:09182:03194:51201:32213:25224:45233:44244:01252:32264:02272:56286:28295:07307:05312:27323:47334:55343:46352:15364:41377:46383:52391:55405:59416:00424:50435:21446:43455:44462:47473:31484:28496:04502:54515:17523:19532:48543:47552:53562:42574:19583:51594:35604:41612:47622:29633:48642:14655:37665:59