[1] Abubuwan da Allah ya yi magana a kai game da Babilon da Ishaya ɗan Amoz ya gani.
[2] A tā da tuta a kan tudun da yake mai fili, ka tā da murya gare su; ka ɗaga hannu ka ba su alama don su shiga ƙofofi masu alfarma.
[3] Na umarci tsarkakana; na umarci jarumawan yaƙina su gamsar da fushina, waɗanda suke farin ciki a nasarata.
[4] Ka saurara, akwai surutu a kan duwatsu, sai ka ce na babban taron jama’a! Ka saurara, akwai hayaniya a cikin mulkoki, sai ka ce al’ummai ne suna ta tattaruwa! Ubangiji Maɗaukaki yana shirya mayaƙa don yaƙi.
[5] Suna zuwa daga ƙasashe masu nesa, daga iyakokin duniya, Ubangiji da kuma fushinsa, zai hallaka dukan ƙasar.
[6] Ku yi ihu, gama ranar Ubangiji ta yi kusa za tă zo kamar hallaka daga Maɗaukaki.
[7] Saboda wannan, hannun kowane mutum zai yi rauni, ƙarfin halin kowane mutum zai kāsa.
[8] Tsoro zai kama su, zafi da azaba za su ci ƙarfinsu; za su yi ta murɗewa kamar mace mai naƙuda. Za su dubi juna a tsorace, fuskokinsu a ɓace.
[9] Duba, ranar Ubangiji tana zuwa, muguwar rana, mai hasala da zafin fushi, don ta mai da ƙasar kango ta kuma hallakar da masu zunubi da suke cikinta.
[10] Taurarin sama da ƙungiyoyinsu ba za su ba da haskensu ba. Rana za tă yi duhu wata kuma ba zai ba da haskensa ba.
[11] Zan hukunta duniya saboda muguntarta, mugaye saboda zunubansu. Zan kawo ƙarshe ga girman kan masu taƙama in kuma ƙasƙantar da ɗaga kan marasa tausayi.
[12] Zan sa mutum yă fi zinariya zalla wuyar samuwa, fiye da zinariyar Ofir wuyan gani.
[13] Saboda haka zan sa sammai su yi rawar jiki; duniya kuma za tă girgiza daga inda take a fushin Ubangiji Maɗaukaki, a ranar fushinsa mai ƙuna.
[14] Kamar barewar da ake farautarta kamar tumaki marasa makiyayi, haka nan kowane mutum zai koma ga mutanensa, kowane mutum zai gudu zuwa ƙasarsa.
[15] Duk wanda aka kama za a soke shi yă mutu; dukan waɗanda aka kama za su mutu ta takobi.
[16] Za a fyaɗa ’ya’yansu a ƙasa su yi kucu-kucu a idanunsu; za a washe gidajensu, a kuma kwana da matansu.
[17] Duba, zan zuga mutanen Medes su yi gāba da su, su da ba su kula da azurfa ba kuma ba sa damuwa da zinariya.
[18] Bakkunansu za su kashe samari; ba za su ji tausayin jarirai ba ba za su kuwa nuna jinƙai ga ’yan yara ba.
[19] Babilon, kayan daraja na mulkoki, abin fariyar Babiloniyawa, Allah zai kaɓantar da ita kamar yadda ya yi da Sodom da Gomorra.
[20] Ba za ƙara kasance da mazauna kuma ba ko a yi zama a cikinta dukan zamanai; Ba wani mutumin Arab da zai kafa tentinsa a can, ba makiyayin da zai taɓa kiwon garkensa a can.
[21] Amma halittun hamada za su kwanta a can, diloli za su cika gidajenta; a can mujiyoyi za su zauna, a can kuma awakin jeji za su yi ta tsalle.
[22] Kuraye za su yi ta kuka a kagarorinta, diloli kuma a cikin fadodinta masu alfarma. Lokacinta ya yi kusa, kwanakinta kuma ba za su yi tsawo ba.