[1] A wannan rana za a rera wannan waƙa a ƙasar Yahuda. Muna da birni mai ƙarfi; Allah yake ceton katanga da kuma kagarunta.
[2] A buɗe ƙofofi saboda al’umma mai adalci ta shiga, al’ummar da mai aminci.
[3] Za ka kiyaye shi da cikakken salama shi wanda ya kafa zuciyarsa gare ka, domin ya dogara a gare ka.
[4] Ku dogara ga Ubangiji, gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.
[5] Yakan ƙasƙantar da waɗanda suke zama a bisa ya kawar da birni mai alfarma ƙasa; ya rusa ta har ƙasa ya jefar da ita cikin ƙura.
[6] Ƙafafu sukan tattake ta, ƙafafu waɗanda aka zalunta, wato, sawun matalauta.
[7] Hanyar masu adalci sumul take; Ya Mai Aikata Gaskiya, ka sa hanyar masu adalci ta yi sumul.
[8] I, Ubangiji, cikin tafiya a hanyar dokokinka, muna sa zuciya gare ka; sunanka da tunani a kanka su ne marmarin zukatanmu.
[9] Raina yana marmarinka da dare; da safe kuma raina yana son ganinka. Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya, mutanen duniya kan koyi adalci.
[10] Ko da yake akan nuna wa mugaye alheri, ba sa koyi adalci; har ma a ƙasar masu aikata gaskiya sukan ci gaba da aikata mugunta ba sa ganin girmar darajar Ubangiji.
[11] Ya Ubangiji an ɗaga hannunka sama, amma ba sa ganinsa. Bari su ga himmarka don mutanenka su kuma sha kunya; bari wutar da aka ajiye don abokan gābanka ta cinye su.
[12] Ubangiji ka kafa salama dominmu; duk abin da muka iya yi kai ne ka yi mana.
[13] Ya Ubangiji, Allahnmu, waɗansu iyayengiji ban da kai sun yi mulki a kanmu, amma sunanka kaɗai muka girmama.
[14] Yanzu duk sun mutu, ba za su ƙara rayuwa ba; waɗannan ruhohin da suka rasu ba za su tashi ba. Ka hukunta su ka kuma kawo su ga hallaka; ka sa ba za a ƙara tunawa da su ba.
[15] Ka fadada al’umma, ya Ubangiji; ka fadada al’umma. Ka samo wa kanka ɗaukaka; ka fadada dukan iyakokin ƙasar.
[16] Ubangiji, sun zo gare ka a cikin damuwarsu; sa’ad da ka hore su, da ƙyar suna iya yin addu’a.
[17] Kamar mace mai ciki da take gab da haihuwa takan yi ta murɗawa tana kuka saboda zafi, haka muka kasance a gabanka, ya Ubangiji.
[18] Muna da ciki, mun yi ta murɗewa saboda zafi, amma mun haifi iska. Ba mu kawo ceto ga duniya ba; ba mu haifi mutanen duniya ba.
[19] Amma matattunka za su rayu; jikunansu za su tashi. Ku da kuke zama a ƙura, ku farka ku kuma yi sowa don farin ciki. Raɓarka kamar raɓar safiya ce; duniya za tă haifi matattunta.
[20] Ku tafi, mutanena, ku shiga ɗakunanku ku kuma kulle ƙofofi; ku ɓoye kanku na ɗan lokaci sai ya huce fushinsa.
[21] Duba, Ubangiji yana fitowa daga mazauninsa don yă hukunta mutanen duniya saboda zunubansu. Duniya za tă bayyana zub da jinin da aka yi a kanta; ba za tă ƙara ɓoye waɗanda aka kashe a cikinta ba.