Listen to this chapter • 1:03
[1] Ga abin da Irmiya annabi ya faɗa wa Baruk ɗan Neriya a shekara ta huɗu ta Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, bayan Baruk ya rubuta maganar da Irmiya ya shibta masa a kan littafi cewa,
[2] “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, yana ce maka, Baruk.
[3] Ka ce, ‘Kaitona! Ubangiji ya ƙara baƙin ciki da wahalata; na gaji da nishe-nishe ban kuma huta ba.’ ”
[4] Ubangiji ya ce, “Ka faɗa masa wannan, ‘Ga abin da Ubangiji yana cewa, zan rushe abin da na gina in kuma tumɓuke abin da na dasa, a duk fāɗin ƙasar.
[5] Ya kamata ka nemi manyan abubuwa wa kanka? Kada ka neme su. Gama zan aukar da masifa a kan dukan mutane, in ji Ubangiji, amma duk inda ka tafi zan bar ka ka kuɓutar da ranka.’ ”
Irmiya — Chapters
12:5827:3335:1645:5555:4265:3176:0784:2594:48104:32115:01123:35135:00144:47154:30164:32175:44184:39193:23203:50213:11226:24238:09242:13257:13264:57274:29283:16296:55304:38318:27328:57335:26344:43354:18366:14373:41385:26393:31404:17413:50424:16432:46447:21451:03465:59471:41488:22497:48509:145111:58527:06