Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:31

[1] A shekara ta tara ta Zedekiya sarkin Yahuda, a wata na goma, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya fita yaƙi da Urushalima da dukan sojojinsa ya kuma yi mata ƙawanya.

[2] A rana ta tara ga watan huɗu a shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya, sai aka huda katanga.

[3] Sa’an nan dukan fadawan sarkin Babilon suka shiga suka zazzauna a Ƙofar Tsakiya. Wato, Nergal-Sharezer na Samgar-Nebo, Sarsekim wani babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da dukan sauran fadawan sarkin Babilon.

[4] Sa’ad da Zedekiya sarkin Yahuda da dukan sojoji suka gan su, sai suka gudu; suka bar birnin da dare ta hanyar lambun sarki, ta ƙofar da take tsakanin katanga biyu, suka nufi waje Araba.

[5] Amma sojojin Babiloniyawa suka bi su, suka ci wa Zedekiya a filayen Yeriko. Suka kama shi suka kai shi wurin Nebukadnezzar a Ribla a ƙasar Hamat, inda aka yanke masa hukunci.

[6] A can Ribla sarkin Babilon ya kashe ’ya’yan Zedekiya a idanunsa aka kuma kashe dukan manyan mutanen Yahuda.

[7] Sa’an nan ya ƙwaƙule idanun Zedekiya ya kuma buga masa ƙuƙumi, ya kai shi Babilon.

[8] Sai Babiloniyawa suka cinna wa fadar da kuma gidajen mutane wuta suka farfasa katangar Urushalima.

[9] Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya kwashi mutanen da suka rage a birnin zuwa zaman bauta a Babilon, tare da waɗanda suka riga suka tafi wurinsa, da kuma sauran mutanen.

[10] Amma Nebuzaradan shugaban matsaran ya bar waɗansu matalauta a ƙasar Yahuda, su da ba su da kome; a lokacin kuwa ya ba su gonakin inabi da kuma filaye.

[11] To, fa, Nebukadnezzar sarkin Babilon ya ba da wannan umarnai game da Irmiya ta wurin Nebuzaradan shugaban matsaran sarki cewa,

[12] “Ka ɗauke shi ka lura da shi da kyau, kada ka yi masa wani mugun abu, amma ka yi masa dukan abin da yake so.”

[13] Saboda haka Nebuzaradan shugaban matsara, Nebushazban babban hafsa, Nergal-Sharezer bafade mai girma da sauran hafsoshin sarkin Babilon

[14] suka aika aka kawo Irmiya daga filin matsar. Suka miƙa shi ga Gedaliya ɗan Ahikam, ɗan Shafan, don yă kai shi gidansa. Saboda haka ya zauna a can a cikin mutanensa.

[15] Yayinda aka kulle Irmiya a sansanin matsara, maganar Ubangiji ta zo masa cewa,

[16] “Tafi ka faɗa wa Ebed-Melek mutumin Kush, ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa ina gab da cika maganata a kan wannan birni ta wurin masifa, ba wadata ba. A lokacin za tă cika a idanunka.

[17] Amma zan kuɓutar da kai a wannan rana, in ji Ubangiji; ba zan ba da kai ga waɗanda kake tsoronsu ba.

[18] Zan cece ka; ba za ka mutu ta wurin takobi ba amma za ka tsira da ranka, domin ka dogara gare ni, in ji Ubangiji.’ ”

Irmiya — Chapters