[1] Da firist nan Fashhur ɗan Immer, babban ma’aikaci a cikin haikalin Ubangiji, ya ji Irmiya yana annabcin waɗannan abubuwa,
[2] sai ya sa aka yi wa Irmiya dūka aka kuma sa shi a turu a Ƙofar Bisa na Benyamin a haikalin Ubangiji.
[3] Kashegari, sa’ad da Fashhur ya fitar da shi daga turu, sai Irmiya ya ce masa, “Ubangiji ba zai kira ka Fashhur ba, amma ya ba ka suna Magor-Missabib.
[4] Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Zan maishe ka abin razana ga kanka da kuma ga dukan abokanka; da idanunka za ka gan takobin abokan gāba yana kashe su. Zan miƙa Yahuda duka ga sarkin Babilon, wanda zai kwashe su zuwa Babilon ya kuma kashe su da takobi.
[5] Zan ba wa abokan gābansu dukan dukiyar wannan birni dukan amfaninsa, dukan abubuwa masu daraja na sarakunan Yahuda. Za su kwashe su ganima su kai su Babilon.
[6] Kai kuma Fashhur, da dukan waɗanda suke a gidanka za ku tafi zaman bauta a Babilon. A can za ku mutu a kuma binne ku, da kai da dukan abokanka waɗanda ka yi musu annabce-annabcen ƙarya.’ ”
[7] Ya Ubangiji, ka ruɗe ni, na kuwa ruɗu; ka fi ni ƙarfi, ka kuwa yi nasara. Na zama abin dariya dukan yini; kowa yana yi mini ba’a.
[8] Duk sa’ad da na yi magana, nakan tā da murya ina furta hargitsi da hallaka. Haka maganar Ubangiji ta kawo mini zagi da reni dukan yini.
[9] Amma in na ce, “Ba zan ambace shi ba ba zan ƙara yin magana da sunansa ba,” sai in ji maganarsa a cikina kamar wuta, wutar da aka kulle a ƙasusuwana. Na gaji da danne ta a cikina; tabbatacce ba zan iya ba.
[10] Na ji mutane da yawa suna raɗa cewa, “Razana ta kowace fuska! Mu kai kararsa! Bari mu kai kararsa!” Dukan abokaina suna jira in yi tuntuɓe, suna cewa, “Mai yiwuwa a ruɗe shi; sai mu yi nasara a kansa mu ɗau fansa a kansa.”
[11] Amma Ubangiji yana tare da ni kamar babban jarumi; saboda haka masu tsananta mini za su yi tuntuɓe ba kuwa za su yi nasara ba. Za su fāɗi su kuma sha mummunar kunya; ba za a taɓa manta da rashin bangirmansu ba.
[12] Ya Ubangiji Maɗaukaki, kai da kake gwada adali kana bincika zuciya duk da tunani, bari in ga sakayyarka a kansu, gama a gare ka na miƙa damuwata.
[13] Ku rera ga Ubangiji! Ku yabi Ubangiji! Ya kuɓutar da ran mabukaci daga hannuwan mugaye.
[14] La’ananniya ce ranar da aka haife ni! Kada ranar da mahaifiyata ta haife ni ta zama mai albarka!
[15] La’ananne ne mutumin da ya kawo wa mahaifina labari, wanda ya sa shi ya yi murna cewa, “An haifa maka yaro, ɗa namiji!”
[16] Bari mutumin ya zama kamar garuruwan da Ubangiji ya tumɓuke ba tausayi. Bari yă ji kuka da safe kururuwan yaƙi kuma da tsakar rana.
[17] Gama bai kashe ni a cikin ciki ba, da ma ya sa cikin mahaifiyata ya zama kabarina, cikinta ya fadada har abada.
[18] Me ya sa na ma fito daga cikin ciki in ga wahala da baƙin ciki in kuma ƙare kwanakina da kunya?