Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:26

[1] Yayinda Irmiya yana a tsare a sansanin matsara, sai maganar Ubangiji ta zo masa sau na biyu cewa,

[2] “Ga abin da Ubangiji yana cewa, shi da ya halicci duniya, Ubangiji wanda ya siffanta ta ya kuma kafa ta, Ubangiji ne sunansa.

[3] ‘Kira gare ni zan kuwa amsa maka in kuma faɗa maka manyan abubuwan da ba a iya kaiwa, da ba ka sani ba.’

[4] Gama ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila yana cewa game da gidaje a wannan birni da fadodin Yahuda da aka rurrushe domin a yi amfani da su a kan mahaurai da kuma takobi

[5] a yaƙi da Babiloniyawa. ‘Za su cika da gawawwakin mutane waɗanda na kashe da fushina da hasalata. Zan ɓoye fuskata wa wannan birni saboda dukan muguntarsu.

[6] “ ‘Duk da haka, zan kawo lafiya da warkarwa gare ta; zan warkar da mutanena in kuma wadata su da salama da zama lafiya.

[7] Zan komo da Yahuda da Isra’ila daga bauta zan kuma sāke gina su kamar yadda suke a dā.

[8] Zan tsarkake su daga dukan zunubin da suka yi mini zan kuma gafarta musu dukan zunubansu na yin mini tawaye.

[9] Sa’an nan birnin nan za tă sa in zama sananne, farin ciki, yabo da girma a gaban dukan al’ummai a duniya da suka ji abubuwa masu kyau da na yi mata; za su kuma yi mamaki su kuma yi rawan jiki saboda yalwar wadata da salamar da na ba ta.’

[10] “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Kuna cewa game da wannan wuri, “Kango ne, babu mutane ko dabbobi.” Duk da haka a cikin garuruwan Yahuda da titunan Urushalima da aka yashe, inda ba mutane ko dabbobi, za a sāke jin

[11] sowa ta farin ciki da murna, muryoyin amarya da na ango, da muryoyin waɗanda suka kawo hadayun salama a gidan Ubangiji suna cewa, “ ‘ “Ku yi godiya ga Ubangiji Maɗaukaki, gama Ubangiji mai alheri ne; ƙaunarsa za tă dawwama har abada.” Gama zan mayar da wadatar ƙasar kamar yadda suke a dā,’ in ji Ubangiji.

[12] “Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, ‘A wannan wuri, kango da babu mutane ko dabbobi, cikin dukan garuruwansa za a sāke kasance da wurin kiwo don makiyaya su hutar da garkunansu.

[13] A cikin garuruwan ƙasar tudu, garuruwan yammancin gindin dutse da na Negeb, a yankin Benyamin, a cikin ƙauyuka kewayen Urushalima da kuma a cikin garuruwan Yahuda, garkuna za su sāke bi a ƙarƙashin hannun mai ƙidayawa,’ in ji Ubangiji.

[14] “ ‘Kwanaki suna zuwa,’ in ji Ubangiji, ‘sa’ad da zan cika alkawarin alheri da na yi wa gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda.

[15] “ ‘A waɗannan kwanaki da kuma a wannan lokaci zan tā da Reshe mai adalci daga zuriyar Dawuda; zai yi abin da yake daidai da kuma gaskiya a ƙasar.

[16] A kwanakin nan zan ceci Yahuda Urushalima kuma za tă zauna lafiya. Sunan da za a kira ta shi ne, Ubangiji Adalcinmu.’

[17] Gama ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘Dawuda ba zai taɓa rasa mutumin da zai zauna a gadon sarautar Isra’ila ba,

[18] ba kuwa firistoci waɗanda suke Lawiyawa za su rasa mutumin da zai ci gaba da tsaya a gabana don miƙa hadayun ƙonawa, ya ƙona hadayun hatsi ya kuma miƙa sadakoki ba.’ ”

[19] Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,

[20] “Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ka tā da alkawarina na rana da kuma alkawarina na dare, har dare da rana ba za su ƙara bayyana a ƙayyadaddun lokutansu ba,

[21] to, sai a tā da alkawarina da Dawuda bawana da alkawarina da Lawiyawan da suke firistoci masu hidima a gabana, Dawuda kuma ba zai ƙara kasance da zuriyar da za tă yi mulki.

[22] Zan sa zuriyar Dawuda bawana da kuma Lawiyawan da suke hidima a gabana su yi yawa kamar taurarin sararin sama da kuma yashin bakin tekun da ba a iya ƙidaya.’ ”

[23] Sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya cewa,

[24] “Ba ka lura ba cewa waɗannan mutane suna cewa, ‘Ubangiji ya ƙi masarautai biyu da ya zaɓa’? Saboda haka suka rena mutanena ba sa ƙara ɗaukansu a matsayin al’umma.

[25] Ga abin da Ubangiji yana cewa, ‘In ban kafa alkawarina game da rana da kuma game da dare ba in kuma gyara dokokin sama da duniya ba,

[26] to zan ƙi zuriyar Yaƙub da na Dawuda bawana ba zan kuma zaɓi ɗaya daga cikin ’ya’yansa maza ya yi mulki a kan zuriyar Ibrahim, Ishaku da Yaƙub ba. Gama zan mayar da wadatarsu in kuma yi musu jinƙai.’ ”

Irmiya — Chapters