Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 8:59

[1] Da sassafe a ranar farko ta mako, matan suka je kabarin, da kayan ƙanshin da suka shirya.

[2] Suka iske an riga an gungurar da dutsen daga bakin kabarin.

[3] Amma da suka shiga ciki, ba su iske jikin Ubangiji Yesu ba.

[4] Yayinda suna cikin tunani a kan wannan, nan take, ga waɗansu mutum biyu tsaye kusa da su, sanye da kaya masu ƙyalli, kamar walƙiya.

[5] A cikin tsoro, matan suka fāɗi da fuskokinsu a ƙasa, amma mutanen suka ce musu, “Me ya sa kuke neman mai rai a cikin matattu?

[6] Ba ya nan, ya tashi! Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana tare da ku a Galili cewa,

[7] ‘Dole a ba da Ɗan Mutum ga hannun masu zunubi, a kuma gicciye shi, a rana ta uku kuma a tashe shi.’ ”

[8] Sai suka tuna da maganarsa.

[9] Da suka dawo daga kabarin, sai suka faɗa wa Sha Ɗayan nan da sauransu, dukan waɗannan abubuwa.

[10] Matan da suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa su ne, Maryamu Magdalin, da Yowanna, da Maryamu uwar Yaƙub, da waɗansu da suke tare da su.

[11] Amma ba su gaskata matan ba, domin sun ɗauki kalmominsu wani zancen banza ne.

[12] Duk da haka, Bitrus ya tashi a guje zuwa kabarin. Da ya sunkuya, sai ya ga ƙyallayen lilin kaɗai a kwance. Sai ya koma yana tunani a ransa, a kan abin da ya faru.

[13] A wannan rana kuma, biyu daga cikinsu suna tafiya zuwa wani ƙauye, da ake kira Emmawus, da suke kusan mil bakwai daga Urushalima.

[14] Suna magana da juna a kan dukan abubuwan da suka faru.

[15] Da suna magana, kuma suna tattauna waɗannan abubuwa da junansu, sai Yesu da kansa ya zo yana tafiya tare da su.

[16] Amma ba a ba su ikon gane shi ba.

[17] Sai ya tambaye, su ya ce, “Mene ne kuke tattaunawa da juna a cikin tafiyarku?” Suka tsaya shiru, da damuwa a fuskarsu.

[18] Ɗaya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya tambaye shi ya ce, “Ashe, kai baƙo ne a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, a cikin kwanakin nan ba?”

[19] Sai ya yi tambaya, “Waɗanne abubuwa?” Suka amsa suka ce, “Game da Yesu Banazare. Shi annabi ne, mai iko ne kuma cikin ayyukansa da maganarsa, a gaban Allah da kuma dukan mutane.

[20] Manyan firistoci da masu mulkinmu sun ba da shi a yi masa hukuncin mutuwa, suka kuwa gicciye shi.

[21] Amma da, muna sa zuciya cewa, shi ne wanda zai fanshi Isra’ila. Bugu da ƙari kuma yau kwana uku ke nan tun da wannan abin ya faru.

[22] Har wa yau, waɗansu daga cikin matanmu sun ba mu mamaki. Sun je kabarin da sassafen nan,

[23] amma ba su sami jikinsa ba. Sun dawo sun faɗa mana cewa, sun ga wahayi na mala’iku, da suka ce yana da rai.

[24] Sa’an nan, waɗansu abokanmu suka je kabarin, suka kuma tarar da kome kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.”

[25] Sai ya ce musu, “Ashe, ku marasa azanci ne, masu nauyin zuciyar gaskata, da dukan abin da annabawa suka faɗa!

[26] Ai, dole Kiristi yă sha waɗannan wahalolin, kafin yă shiga ɗaukakarsa.

[27] Sai ya fara bayyana musu daga Musa da dukan Annabawa, abin da dukan Nassi ya faɗa a kansa.”

[28] Da suka yi kusa da ƙauyen da za su, sai Yesu ya yi kamar zai ci gaba.

[29] Amma suka matsa masa suka ce, “Sauka wurinmu, don dare ya kusa, rana ta kusa fāɗuwa.” Sai ya sauka wurinsu.

[30] Da ya zauna a tebur tare da su, sai ya ɗauki burodi, ya yi godiya, ya kakkarya ya fara ba su.

[31] Sa’an nan idanunsu suka buɗe, suka gane shi. Sai ya ɓace musu.

[32] Suka tambayi juna, “Ashe, shi ya sa zukatanmu suka kuna a cikinmu, sa’ad da yake magana da mu a hanya, yana bayyana mana Nassi.”

[33] Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. A can suka sami Sha Ɗayan nan da waɗanda suke tare da su a wuri ɗaya,

[34] suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman”

[35] Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin.

[36] Suna cikin wannan zance, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu. Sai ya ce musu, “Salama a gare ku!”

[37] Suka firgita, suka tsorota, suna tsammani fatalwa ce suka gani.

[38] Sai ya ce musu, “Don me kuke damuwa, kuke kuma shakka a zuciyarku?

[39] Ku duba hannuwana da ƙafafuna. Ai, ni ne da kaina! Ku taɓa ni ku ji, ai, fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.”

[40] Da ya faɗi haka, sai ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa.

[41] Kuma har yanzu, suna cikin rashin gaskatawa, saboda murna da mamaki, sai ya tambaye su, “Kuna da abinci a nan?”

[42] Suka ba shi ɗan gasasshen kifi,

[43] ya karɓa ya ci a gabansu.

[44] Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da na gaya muku tun ina tare da ku cewa, dole a cika kome da aka rubuta game da ni, a cikin Dokar Musa, da Annabawa, da kuma Zabura.”

[45] Sai ya wayar da tunaninsu don su fahimci Nassi.

[46] Ya ce musu, “Wannan shi ne abin da aka rubuta, cewa dole Kiristi yă sha wahala, a rana ta uku kuma yă tashi daga matattu.

[47] Kuma a cikin sunansa za a yi wa’azin tuba da gafarar zunubai, ga dukan ƙasashe. Za a kuwa fara daga Urushalima.

[48] Ku ne shaidun waɗannan abubuwa.

[49] Zan aika muku da abin da Ubana ya yi alkawari. Amma ku dakata a birnin tukuna, sai an rufe ku da iko daga sama.”

[50] Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka.

[51] Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.

[52] Sai suka yi masa sujada, suka koma Urushalima cike da murna sosai.

[53] Sai suka ci gaba da zama a cikin haikalin, suna yabon Allah.

Luka — Chapters