Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 9:10

[1] A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma.

[2] (Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.)

[3] Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.

[4] Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne.

[5] Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.

[6] Yayinda suke can, sai lokacin haihuwar jaririn ya yi,

[7] ta kuwa haifi ɗanta na fari. Ta nannaɗe shi a zane ta kuma kwantar da shi cikin wani kwami, don ba su sami ɗaki a masauƙi ba.

[8] Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare.

[9] Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai.

[10] Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.

[11] Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.

[12] Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”

[13] Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa,

[14] “Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”

[15] Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.”

[16] Sai suka tafi da sauri, suka tarar da Maryamu da Yusuf, da kuma jaririn kwance a kwami.

[17] Sa’ad da suka gan shi, sai suka baza maganar da aka gaya musu game da yaron,

[18] duk kuwa waɗanda suka ji wannan, suka yi mamaki a kan abin da makiyayan suka faɗa.

[19] Amma Maryamu ta riƙe dukan waɗannan abubuwa ta kuma yi ta tunaninsu a zuciyarta.

[20] Makiyayan kuwa suka koma, suna ɗaukaka suna kuma yabon Allah saboda dukan abubuwan da suka ji, suka kuma gani, yadda aka gaya musu.

[21] A rana ta takwas, da lokaci ya yi da za a yi masa kaciya, sai aka ba shi suna Yesu, sunan da mala’ika ya ba shi kafin a yi cikinsa.

[22] Da lokacin tsarkakewarsu bisa ga Dokar Musa ya cika, sai Yusuf da Maryamu suka ɗauke shi suka haura zuwa Urushalima don su miƙa shi ga Ubangiji

[23] (yadda yake a rubuce a Dokar Ubangiji cewa, “Kowane ɗan fari, za a keɓe shi ga Ubangiji”),

[24] don kuma su miƙa hadaya bisa ga abin da aka faɗa a Dokar Ubangiji cewa, “kurciyoyi biyu ko ’yan tattabarai biyu.”

[25] To, akwai wani mutum a Urushalima mai suna Siman, shi mai adalci da kuma mai ibada. Yana jiran fansar Isra’ila, Ruhu Mai Tsarki kuwa yana tare da shi.

[26] An bayyana masa ta wurin Ruhu Mai Tsarki cewa ba zai mutu ba sai ya ga Kiristi na Ubangiji.

[27] Da Ruhu ya iza shi, sai ya shiga cikin filin haikali. Sa’ad da iyayen suka kawo jaririn nan Yesu don su yi masa abin da al’adar Doka ta bukaci,

[28] sai Siman ya karɓi yaron a hannuwansa ya yabi Allah, yana cewa,

[29] “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, kamar yadda ka yi alkawari, yanzu ka sallami bawanka lafiya.

[30] Gama idanuna sun ga cetonka,

[31] wanda ka shirya a gaban dukan mutane,

[32] haske don bayyanawa ga Al’ummai da kuma ɗaukaka ga mutanenka Isra’ila.”

[33] Mahaifin yaron da kuma mahaifiyarsa suka yi mamaki abin da aka faɗa game da shi.

[34] Sa’an nan Siman ya sa musu albarka ya ce wa Maryamu mahaifiyarsa, “An ƙaddara yaron nan yă zama sanadin fāɗuwa da tashin mutane da yawa a Isra’ila, zai kuma zama alamar da mutane ba za su so ba,

[35] ta haka za a fallasa tunanin zukatan mutane da yawa. Ke ma, takobi zai soki zuciyarki.”

[36] Akwai wata annabiya ma, mai suna Anna, diyar Fanuwel, na kabilar Asher. Ta tsufa kutuf; ta yi zama da mijinta shekaru bakwai bayan sun yi aure,

[37] ta kuwa zama gwauruwa sai da ta kai shekaru tamanin da huɗu. Ba ta taɓa barin haikali ba, tana sujada dare da rana, tana kuma azumi da addu’a.

[38] Tana haurawa wurinsu ke nan a wannan lokaci, sai ta yi wa Allah godiya ta kuma yi magana game da yaron nan ga dukan waɗanda suke sauraron fansar Urushalima.

[39] Bayan da Yusuf da Maryamu suka gama yin dukan abubuwan da Dokar Ubangiji ta bukaci, sai suka koma Galili suka tafi Nazaret garinsu.

[40] Yaron kuwa ya yi girma ya yi ƙarfi; ya cika da hikima, alherin Allah kuwa yana bisansa.

[41] Kowace shekara, iyayen Yesu sukan je Urushalima don Bikin Ƙetarewa.

[42] Da Yesu ya cika shekaru goma sha biyu, sai suka tafi Bikin bisa ga al’ada.

[43] Bayan Bikin, da iyayen suka kama hanya don su koma gida, sai Yesu, yaron nan, ya tsaya a Urushalima, ba da saninsu ba.

[44] Su kuwa sun ɗauka yana tare da su, saboda haka, suka yi ta tafiya har na yini guda. Sa’an nan suka fara nemansa cikin ’yan’uwansu da abokansu.

[45] Da ba su gan shi ba, sai suka koma Urushalima nemansa.

[46] Bayan kwana uku, sai suka same shi a filin haikali zaune a tsakiyar malamai, yana sauraronsu yana kuma yi musu tambayoyi.

[47] Dukan waɗanda suka ji shi, suka yi mamakin fahimtarsa, da amsoshinsa.

[48] Da iyayensa suka gan shi sai suka yi mamaki. Mahaifiyarsa ta ce masa, “Ɗana, don me ka yi mana haka? Ni da mahaifinka duk mun damu muna nemanka.”

[49] Sai ya ce, “Don me kuke nemana? Ba ku san cewa, dole in kasance a gidan Ubana ba?”

[50] Amma ba su fahimci abin da yake faɗin musu ba.

[51] Sai ya koma Nazaret tare da su, yana yi musu biyayya. Mahaifiyarsa kuma ta riƙe dukan waɗannan abubuwa a zuciyarta.

[52] Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.

Luka — Chapters