Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 12:50

[1] Mutane da yawa sun ɗau niyyar rubuta labarin abubuwan da aka cika a cikinmu,

[2] kamar yadda muka karɓe su daga waɗanda tun farko shaidu ne da kuma masu hidimar bishara.

[3] Saboda haka, da yake ni da kaina na binciko kome a hankali daga farko, na ga ya yi kyau in rubuta maka labarin dalla-dalla, ya mafifici Tiyofilus,

[4] don ka san tabbacin abubuwan da aka koyar da kai.

[5] A lokacin da Hiridus ne yake sarautar Yahudiya, an yi wani firist mai suna Zakariya, na sashin firistoci gidan Abiya. Matarsa Elizabet ma ’yar zuriyar Haruna ce.

[6] Dukansu biyu kuwa masu adalci ne a gaban Allah, suna kuma bin umarnan Ubangiji da farillansa duka da halin rashin zargi.

[7] Sai dai ba su da ’ya’ya, domin Elizabet bakararriya ce; kuma dukansu biyu sun tsufa.

[8] Wata rana da lokacin aikin firistoci na sashen Zakariya na yin hidima ya kewayo, yana kuma cikin hidimarsa ta firist a gaban Allah,

[9] sai aka zaɓe shi ta wurin ƙuri’a, bisa ga al’adar aikin firist, yă shiga haikalin Ubangiji yă ƙone turare.

[10] Da lokacin ƙone turare ya yi, duk taron masu sujada suna a waje suna addu’a.

[11] Sai mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare shi, tsaye a dama da bagaden turare.

[12] Da Zakariya ya gan shi sai ya firgita, tsoro kuma ya kama shi.

[13] Amma mala’ikan ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, Zakariya; an ji addu’arka. Matarka Elizabet za tă haifa maka ɗa, za ka kuma ba shi suna Yohanna.

[14] Zai zama abin murna da farin ciki a gare ka, mutane da yawa kuwa za su yi murna don haihuwarsa,

[15] gama zai zama mai girma a gaban Ubangiji. Ba kuwa zai taɓa shan ruwan inabi ko wani abu mai sa maye ba. Zai cika da Ruhu Mai Tsarki tun haihuwa.

[16] Shi ne zai juye mutanen Isra’ila da yawa zuwa wurin Ubangiji Allahnsu.

[17] Zai sha gaban Ubangiji, a ruhu da kuma iko irin na Iliya, domin yă juye zukatan iyaye ga ’ya’yansu, marasa biyayya kuma ga zama masu biyayya don yă kintsa mutane su zama shiryayyu domin Ubangiji.”

[18] Sai Zakariya ya tambayi mala’ikan ya ce, “Yaya zan tabbatar da wannan? Ga ni tsoho, matana kuma ta kwana biyu.”

[19] Mala’ikan ya ce, “Ni ne Jibra’ilu. Ina tsaya a gaban Allah, an kuma aiko ni in yi maka magana, in kuma faɗa maka wannan labari mai daɗi.

[20] Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.”

[21] Ana cikin haka, mutane suna jiran Zakariya, suna kuma mamaki me ya sa ya daɗe haka a cikin haikali.

[22] Da ya fito, bai iya yin musu magana ba. Sai suka gane, ya ga wahayi ne a haikali, domin ya dinga yin musu alamu, amma ya kāsa yin magana.

[23] Da lokacin hidimarsa ya cika, sai ya koma gida.

[24] Bayan wannan, matarsa Elizabet ta yi ciki, ta kuma riƙa ɓuya har wata biyar.

[25] Sai ta ce, “Ubangiji ne ya yi mini wannan. A waɗannan kwanaki ya nuna tagomashinsa ya kuma kawar mini da kunya a cikin mutane.”

[26] A wata na shida, sai Allah ya aiki mala’ika Jibra’ilu zuwa Nazaret, wani gari a Galili,

[27] gun wata budurwar da aka yi alkawarin aurenta ga wani mutum mai suna Yusuf daga zuriyar Dawuda. Sunan budurwar Maryamu.

[28] Mala’ikan ya je wurinta ya ce, “A gaishe ki, ya ke da kika sami tagomashi ƙwarai! Ubangiji yana tare da ke.”

[29] Maryamu ta damu ƙwarai da kalmominsa, tana tunani wace irin gaisuwa ce haka?

[30] Amma mala’ikan ya ce mata, “Kada ki ji tsoro, Maryamu, kin sami tagomashi a wurin Allah.

[31] Ga shi za ki yi ciki ki kuma haifi ɗa, za ki kuma ba shi suna Yesu.

[32] Zai zama mai girma, za a kuma kira shi Ɗan Maɗaukaki. Ubangiji Allah zai ba shi gadon sarautar kakansa Dawuda,

[33] zai yi mulkin gidan Yaƙub har abada, mulkinsa kuma ba zai taɓa ƙare ba.”

[34] Maryamu ta tambayi mala’ikan ta ce, “Yaya wannan zai yiwu, da yake ni budurwa ce?”

[35] Mala’ikan ya amsa ya ce, “Ruhu Mai Tsarki zai sauko miki, ikon Maɗaukaki kuma zai rufe ke. Saboda haka, Mai Tsarkin nan da za a haifa, za a kira shi Ɗan Allah.

[36] ’Yar’uwarki Elizabet ma za tă haifi ɗa a tsufanta, ita da aka ce bakararriya, ga shi tana a watanta na shida.

[37] Gama ba abin da zai gagari Allah.”

[38] Maryamu ta amsa ta ce, “To, ni baiwar Allah ce, bari yă zama mini kamar yadda ka faɗa.” Sai mala’ikan ya tafi abinsa.

[39] A lokacin sai Maryamu ta shirya ta gaggauta zuwa wani gari a ƙasar tudu ta Yahudiya,

[40] inda ta shiga gidan Zakariya ta kuma gai da Elizabet.

[41] Da Elizabet ta ji gaisuwar Maryamu, sai jaririn da yake a cikinta ya yi motsi. Elizabet kuma ta cika da Ruhu Mai Tsarki.

[42] Sai ta ɗaga murya da ƙarfi ta ce, “Ke mai albarka ce a cikin mata. Mai albarka ne kuma ɗan da za ki haifa!

[43] Me ya sa na sami wannan tagomashi har da mahaifiyar Ubangijina za tă zo wurina?

[44] Da jin gaisuwarki, sai jaririn da yake cikina ya yi motsi don murna.

[45] Mai albarka ce wadda ta gaskata cewa abin da Ubangiji ya faɗa mata zai cika!”

[46] Sai Maryamu ta ce, “Raina yana ɗaukaka Ubangiji

[47] ruhuna kuma yana farin ciki da Allah Mai Cetona,

[48] gama ya lura da ƙasƙancin baiwarsa. Daga yanzu nan gaba dukan zamanai za su ce da ni mai albarka,

[49] gama Mai Iko Duka ya yi mini manyan abubuwa, sunansa labudda Mai Tsarki ne.

[50] Jinƙansa ya kai ga masu tsoronsa, daga zamani zuwa zamani.

[51] Ya aikata manyan ayyuka da hannunsa; ya watsar da waɗanda suke masu girman kai a zurfin tunaninsu.

[52] Ya saukar da masu mulki daga gadajen sarautarsu amma ya ɗaukaka ƙasƙantattu.

[53] Ya ƙosar da masu yunwa da kyawawan abubuwa amma ya sallami mawadata hannu wofi.

[54] Ya taimaki bawansa Isra’ila, yana tunawa yă nuna jinƙai

[55] ga Ibrahim da zuriyarsa har abada, kamar yadda ya faɗa wa kakanninmu.”

[56] Maryamu ta zauna da Elizabet kusan wata uku sa’an nan ta koma gida.

[57] Sa’ad da kwanaki suka yi don Elizabet ta haihu, sai ta haifi ɗa.

[58] Maƙwabtanta da ’yan’uwanta suka ji cewa Ubangiji ya nuna mata jinƙai mai yawa, suka kuma taya ta farin ciki.

[59] A rana ta takwas, sai suka zo don a yi wa yaron kaciya, dā za su sa masa sunan mahaifinsa Zakariya ne,

[60] amma mahaifiyar yaron ta ce, “A’a! Za a ce da shi Yohanna.”

[61] Sai suka ce mata, “Ba wani a cikin danginku mai wannan suna.”

[62] Sai suka yi alamu wa mahaifinsa, don su san sunan da zai su a kira yaron.

[63] Ya yi alama a kawo masa allo, a gaban kowa sai ya rubuta, “Sunansa Yohanna.” Dukan mutane kuwa suka yi mamaki.

[64] Nan da nan bakinsa ya buɗe harshensa kuma ya saku, sai ya fara magana yana yabon Allah.

[65] Maƙwabta duk suka cika da tsoro, mutane kuwa suka yi ta yin magana game da dukan waɗannan abubuwa a ko’ina a cikin ƙasar tudu ta Yahudiya.

[66] Duk waɗanda suka ji wannan kuwa sun yi mamaki suna cewa, “To, me yaron nan zai zama?” Gama hannun Ubangiji yana tare da shi.

[67] Mahaifinsa Zakariya ya cika da Ruhu Mai Tsarki sai ya yi annabci ya ce,

[68] “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, domin ya zo ya kuma fanshe mutanensa.

[69] Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda

[70] (yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),

[71] cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu

[72] don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,

[73] rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,

[74] don yă kuɓutar da mu daga hannun abokan gābanmu, yă kuma sa mu iya yin masa hidima babu tsoro,

[75] cikin tsarki da adalci a gabansa dukan kwanakinmu.

[76] “Kai kuma, ɗana, za a ce da kai annabin Maɗaukaki; gama za ka sha gaban Ubangiji don ka shirya masa hanya,

[77] don ka sanar da mutanensa ceto, ta wurin gafarar zunubansu,

[78] saboda jinƙai na Allahnmu mai ƙauna, hasken nan na ceto zai ɓullo mana daga sama,

[79] don yă haskaka a kan waɗanda suke zama cikin duhu, da kuma cikin inuwar mutuwa, don yă bi da ƙafafunmu a hanyar salama.”

[80] Yaron kuwa ya yi girma ya kuma ƙarfafa a ruhu; ya zauna a hamada sai lokacin da ya fito a fili ga mutanen Isra’ila.

Luka — Chapters