[1] Ubangiji ya ce wa Musa,
[2] “Yi wa taron jama’ar Isra’ila gaba ɗaya magana, ka ce musu, ‘Ku zama masu tsarki, domin Ni, Ubangiji Allahnku, mai tsarki ne.
[3] “ ‘Dole kowannenku yă girmama mahaifiyarsa da mahaifinsa, dole kuma ku kiyaye Asabbacina. Ni ne Ubangiji Allahnku.
[4] “ ‘Kada ku juyo ga gumaka, ko ku yi wa kanku allolin da aka yi zubi da ƙarfe. Ni ne Ubangiji Allahnku.
[5] “ ‘Sa’ad da kuka miƙa hadaya ta salama ga Ubangiji, ku miƙa ta yadda za tă karɓu a madadinku.
[6] Za a ci ta a ranar da kuka miƙa ta, ko kuwa a kashegarin; duk abin da ya rage har kwana ta uku dole a ƙone shi.
[7] In aka ci ta a rana ta uku, marar tsabta ce, ba kuma za a karɓe ta ba.
[8] Duk wanda ya ci ta zai zama da laifi domin ya ƙazantar da abin da yake da tsarki ga Ubangiji, dole a raba mutumin nan da mutanensa.
[9] “ ‘Sa’ad da kuka yi girbin amfanin gonarku, kada ku girbe har zuwa gefen gonar, ko ku yi kalan girbinku.
[10] Kada ku koma gonar inabinku kuna kala, ko ku tattara ’ya’yan inabin da suka fāffāɗi. Ku bar su domin matalauta da kuma baƙi. Ni ne Ubangiji Allahnku.
[11] “ ‘Kada ku yi sata. “ ‘Kada ku yi ƙarya. “ ‘Kada ku ruɗe juna.
[12] “ ‘Kada ku rantse bisa ƙarya da sunana, ta haka har ku ƙasƙantar da sunan Allahnku. Ni ne Ubangiji.
[13] “ ‘Kada ku zalunci maƙwabcinku, ko ku yi masa ƙwace. “ ‘Kada ku riƙe albashin ma’aikaci yă kwana.
[14] “ ‘Kada ku zagi kurma, ko ku sa abin tuntuɓe a gaban makaho, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji.
[15] “ ‘Kada ku yi rashin adalci cikin shari’a; kada ku nuna sonkai ga matalauci, ko ku goyi bayan mai arziki, amma ku shari’anta maƙwabci cikin gaskiya.
[16] “ ‘Kada ku yi ta yawo kuna yaɗa ƙarya a cikin mutanenku. “ ‘Kada ku yi wani abin da zai sa ran maƙwabcinku cikin hatsari. Ni ne Ubangiji.
[17] “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.
[18] “ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.
[19] “ ‘Ku kiyaye farillaina. “ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
[20] “ ‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a ’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a ’yantar da ita ba.
[21] Dole mutumin da ya kwana da ita yă kawo rago a ƙofar Tentin Sujada domin hadaya don laifi ga Ubangiji.
[22] Da ragon hadaya don laifin ne firist zai yi kafara saboda mutumin a gaban Ubangiji saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta zunubinsa.
[23] “ ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai ’ya’ya na ci, ku ɗauki ’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci. Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba.
[24] A shekara ta huɗu, dukan ’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji.
[25] Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin ’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku.
[26] “ ‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa. “ ‘Kada ku yi duba ko sihiri.
[27] “ ‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku.
[28] “ ‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji.
[29] “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta.
[30] “ ‘Ku kiyaye Asabbacina, ku kuma girmama wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji.
[31] “ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
[32] “ ‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.
[33] “ ‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi.
[34] Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
[35] “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu.
[36] Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
[37] “ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’ ”