Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:36

[1] Ubangiji ya ce wa Musa,

[2] “Yi magana da Haruna da ’ya’yansa maza da kuma dukan Isra’ilawa, ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji ya umarta.

[3] Duk mutumin Isra’ilan da ya yanka sa, ɗan rago ko akuya a sansani ko waje da shi

[4] a maimakon kawo shi a matsayin hadaya ga Ubangiji a gaban tabanakul na Ubangiji, za a ɗauki wannan mutum a matsayi mai laifin zub da jini, ya zub da jini, kuma dole a raba shi da mutanensa.

[5] Wannan ya zama haka saboda Isra’ilawa su kawo wa Ubangiji hadayun da suke yi a filaye. Dole su kawo su ga firist, wato, ga Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, su miƙa su a matsayin hadayun salama.

[6] Firist zai yayyafa jinin a bagaden Ubangiji, a ƙofar Tentin Sujada, yă kuma ƙone kitsen kamar ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji.

[7] Kada kuma su ƙara yin hadayunsu ga gumaka masu siffar bunsurai waɗanda suka bauta wa. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare su wa tsararraki masu zuwa.’

[8] “Faɗa musu, ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko wani baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya miƙa hadaya ta ƙonawa ko sadaka

[9] kuma bai kawo shi a ƙofar Tentin Sujada don yă miƙa shi ga Ubangiji ba, dole a raba wannan mutum da mutanensa.

[10] “ ‘Duk mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinsu wanda ya ci wani jini, zan yi gāba da wannan mutum wanda ya ci jinin, za a kuma raba shi da mutanensa.

[11] Gama ran halitta yana a cikin jinin, kuma na ba da shi gare ku don kafara a kan bagade, jini ne yake kafara saboda ran mutum.

[12] Saboda haka na ce wa Isra’ilawa, “Babu waninku da zai ci jini, babu wani baƙon da yake zama a cikinku da zai ci jini.”

[13] “ ‘Duk wani mutumin Isra’ila ko baƙon da yake zama a cikinku wanda ya ji wa wani dabba ko tsuntsu wanda ake ci ciwo, dole yă tsiyaye jinin yă rufe shi da ƙasa,

[14] domin ran kowace halitta yana cikin jini. Shi ya sa na ce wa Isra’ilawa, “Kada ku ci jinin wani halitta, domin ran kowace halitta yana cikin jinin; duk wanda ya ci shi dole a fid da shi.”

[15] “ ‘Kowa, ko haifaffe ɗan ƙasa ko baƙo, da ya ci wani abin da aka sami a mace, ko naman jeji ya yayyage, dole yă wanke rigunansa, yă kuma yi wanka, zai kuma ƙazantu har yamma; sa’an nan zai tsarkake.

[16] Amma in bai wanke rigunansa ya kuma yi wanka ba, alhaki zai kasance a kansa.’ ”

Firistoci — Chapters