[1] Ubangiji ya ce wa Musa,
[2] “Yi wa Isra’ilawa magana ka kuma faɗa musu cewa, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku.
[3] Kada ku yi yadda suke yi a Masar inda da kuke zama, kuma ba a ku yi kamar yadda suke yi a ƙasar Kan’ana inda nake kawo ku ba. Kada ku yi yadda suke yin abubuwa.
[4] Dole ku kiyaye dokokina kuma ku lura ku bi farillaina. Ni ne Ubangiji Allahnku.
[5] Ku kiyaye farillaina da dokokina, gama mutumin da ya aikata waɗannan abubuwa zai rayu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji.
[6] “ ‘Kada wani ya kusaci wani dangi na kusa don yă yi jima’i. Ni ne Ubangiji.
[7] “ ‘Kada ka ƙasƙantar da mahaifinka ta wurin kwana da mahaifiyarka. Ita mahaifiyarka ce; kada ka yi jima’i da ita.
[8] “ ‘Kada ka yi jima’i da matar mahaifinka, wannan zai ƙasƙantar da mahaifinka.
[9] “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwarka, ko ’yar mahaifinka ko ’yar mahaifiyarka, ko an haife ta a gida ɗaya da kai ko kuwa a wani wuri dabam.
[10] “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanka ko ’yar ’yarka, wannan zai ƙasƙantar da kai.
[11] “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar matar mahaifinka wadda aka haifa wa mahaifinka; ita ’yar’uwarka ce.
[12] “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifinka, ita dangin mahaifinka ne na kusa.
[13] “ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, domin ita dangin mahaifiyarka ce na kusa.
[14] “ ‘Kada ka ƙasƙantar da ɗan’uwan mahaifinka ta wurin kusaci matarsa don ka yi jima’i da ita, ita bābarka ce.
[15] “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗanka. Ita matar ɗanka ne; kada ka yi jima’i da ita.
[16] “ ‘Kada ka yi jima’i da matar ɗan’uwanka; wannan zai ƙasƙanta ɗan’uwanka.
[17] “ ‘Kada ka yi jima’i da mace da kuma ’yarta. Kada ka yi jima’i da ’yar ɗanta ko ’yar ’yarta; su danginta ne na kusa. Wannan mugun abu ne.
[18] “ ‘Kada ka auri ’yar’uwar matarka ta zama kishiyar matarka ka kuma yi jima’i da ita yayinda matarka tana da rai.
[19] “ ‘Kada ka kusaci mace don ka yi jima’i da ita a lokacin ƙazantar al’adarta.
[20] “ ‘Kada ka yi jima’i da matar maƙwabcinka ka ƙazantar da kanka tare da ita.
[21] “ ‘Kada ku ba da wani daga cikin ’ya’yanku don a yi hadaya wa Molek, gama ba za ku ƙasƙantar da sunan Allahnku ba. Ni ne Ubangiji.
[22] “ ‘Kada ka kwana da namiji kamar yadda namiji yakan kwana da ta mace, wannan abin ƙyama ne.
[23] “ ‘Kada ka yi jima’i da dabba ka ƙazantar da kanka. Mace ba za tă ba da kanta ga dabba don yă yi jima’i da ita ba; wannan abin ƙyama ne.
[24] “ ‘Kada ku ƙazantar da kanku da wani daga cikin waɗannan, domin haka al’umman da zan kora a gabanku suka ƙazantu.
[25] Har ƙasar ma ta ƙazantu, saboda haka na hukunta ta saboda zunubinta, ƙasar kuwa ta amayar da mazaunanta.
[26] Amma dole ku kiyaye farillaina da kuma dokokina. Kada haifaffe ɗan ƙasa da baƙin da suke zama a cikinku yă yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama,
[27] gama mutanen da suka zauna a wannan ƙasa kafin ku sun aikata dukan waɗannan abubuwa, suka kuma ƙazantu.
[28] Kuma in kuka ƙazantar da ƙasar, za tă amayar da ku kamar yadda ta amayar da al’umman da suka riga ku.
[29] “ ‘Duk wanda ya yi wani daga cikin waɗannan abubuwa banƙyama, dole a fid da mutumin daga cikin mutanensa.
[30] Ku kiyaye umarnaina kuma kada yi ku wata al’ada mai banƙyamar da aka yi kafin ku zo kuma kada ku ƙazantar da kanku da su. Ni ne Ubangiji Allahnku.’ ”