Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:41

[1] a duka sa’ad da zan warkar da Isra’ila, zunuban Efraim za su tonu za a kuma bayyana laifofin Samariya. Suna ruɗu, ɓarayi sukan fasa su shiga gidaje, ’yan fashi sukan yi fashi a tituna;

[2] amma ba su gane cewa na tuna da dukan ayyukan muguntarsu ba. Zunubansu sun kewaye su; kullum suna a gabana.

[3] “Suna faranta wa sarki zuciya da muguntarsu, shugabanni kuma da ƙarairayinsu.

[4] Dukansu mazinata ne suna ƙuna kamar matoya wadda mai gashin burodi ba ya bukata yă tura mata wuta daga cuɗe kullu har kumburinsa.

[5] A ranar bikin sarkinmu shugabanni sukan bugu da ruwan inabi, yă yi cuɗanya da masu ba’a.

[6] Zukatansu suna kamar matoya; sukan kusace shi da wayo. Muguwar aniyarsu takan yi ta ci dukan dare; da safe sai ta ƙuna kamar harshen wuta.

[7] Dukansu suna da zafi kamar matoya; suna kashe masu mulkinsu. Dukan sarakunansu sukan fāɗi, kuma babu waninsu da yake kira gare ni.

[8] “Efraim yana cuɗanya da al’ummai; Efraim waina ne mai fāɗi da ba a juye ba.

[9] Baƙi sun tsotse ƙarfinsa, amma bai gane ba. Gashi kansa ya cika da furfura, amma bai lura ba.

[10] Girmankan Isra’ila ya ba da shaida a kansa, amma duk da haka bai dawo ga Ubangiji Allahnsa ko yă neme shi ba.

[11] “Efraim yana kama da kurciya, marar wayo, marar hankali, yanzu yana kira ga Masar, yanzu yana juyewa ga Assuriya.

[12] Sa’ad da suka tafi, zan jefa ragata a kansu; zai janye su ƙasa kamar tsuntsayen sararin sama. Sa’ad da na ji suna tafiya tare, zan kama su.

[13] Kaitonsu, domin sun kauce daga gare ni! Hallaka za tă aukar musu, domin sun tayar mini! Na ƙudura in cece su amma suna faɗar ƙarya a kaina.

[14] Ba sa yin mini kuka da zuciyarsu amma suna ihu a kan gadajensu. Sukan taru wurin ɗaya don hatsi da ruwan inabi amma su juya mini baya.

[15] Na horar da su na kuma ƙarfafa su, amma sun ƙulla mini maƙarƙashiya.

[16] Ba sa juya ga Mafi Ɗaukaka; suna kama da tanƙwararren baka. Za a kashe shugabanninsu da takobi saboda banzan maganganunsu. Saboda wannan za a wulaƙanta su a ƙasar Masar.

Hosiya — Chapters