Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:58

[1] Efraim yana kiwo a kan iska; yana fafarar iskar gabas dukan yini yana riɓaɓɓanya ƙarairayi da rikici. Ya yi yarjejjeniya da Assuriya ya kuma aika wa Masar man zaitun.

[2] Ubangiji yana da ƙarar da zai kawo a kan Yahuda; zai hukunta Yaƙub bisa ga hanyoyinsa zai sāka masa bisa ga ayyukansa.

[3] A cikin mahaifa ya cafke ɗiɗɗigen ɗan’uwansa; a matsayin mutum ya yi kokawa da Allah.

[4] Ya yi kokawa da mala’ika ya kuma rinjaye shi; ya yi kuka ya kuma yi roƙo don tagomashi. Ya same shi a Betel ya kuma yi magana da shi a can,

[5] Ubangiji Allah Maɗaukaki, Ubangiji ne sunansa sananne!

[6] Amma dole ku koma ga Allahnku; ku ci gaba da ƙauna da yin gaskiya, ku kuma saurari Allahnku kullum.

[7] Ɗan kasuwa yana amfani da mudu marar gaskiya; yana jin daɗin cuta.

[8] Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”

[9] “Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar; zan sa ku sāke zauna a tentuna, kamar a kwanakin ƙayyadaddun bukukkuwanku.

[10] Na yi magana da annabawa, na ba su wahayi da yawa na kuma ba da misalai ta wurinsu.”

[11] Gileyad mugu ne? Mutanensa mutanen banza ne! Suna miƙa bijimai a Gilgal? Bagadansu za su zama tsibin duwatsu. A gonar da aka nome.

[12] Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram; Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata, domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki.

[13] Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar ta wurin annabi ya lura da shi.

[14] Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi; shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.

Hosiya — Chapters