Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:14

[1] “Ku zo, mu koma ga Ubangiji. Ya yayyage mu kucu-kucu amma zai warkar da mu; ya ji mana ciwo amma zai daure mana miyakunmu.

[2] Bayan kwana biyu zai rayar da mu, a rana ta uku zai tashe mu, don mu rayu a gabansa.

[3] Bari mu yarda da Ubangiji; bari mu nace gaba don mu yarda da shi. Muddin rana tana fitowa, zai bayyana; zai zo mana kamar ruwan bazara, kamar ruwan saman farko da yake jiƙe ƙasa.”

[4] “Me zan yi da kai Efraim? Me zan yi da kai Yahuda? Ƙaunarku tana kamar hazon safiya, kamar raɓar safiya da takan ɓace.

[5] Saboda haka na yayyaga ku kucu-kucu tare da annabawana, na kashe ku da kalmomin bakina; hukuntaina sun haskaka kamar walƙiya a kanku.

[6] Gama jinƙai nake bukata, ba hadaya ba, ku kuma san Allah a maimakon hadayun ƙonawa.

[7] Kamar Adamu, sun tā da alkawari, sun yi mini rashin aminci a can.

[8] Gileyad birni ce ta mugayen mutane, da tabon alamun jini.

[9] Kamar yadda mafasa sukan yi fakon mutum, haka ƙungiyoyin firistoci suke; suna kisa a hanya zuwa Shekem, suna aikata laifofi bankunya.

[10] Na ga wani abu mai bantsoro a gidan Isra’ila. A can Efraim ya miƙa wuya ga karuwanci Isra’ila kuma ta ƙazantu.

[11] “Ku kuma, ya mutanen Yahuda, na shirya muku ranar girbi. “A duk sa’ad da zan mayar da dukiya wa mutanena,

Hosiya — Chapters