Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:00

[1] Addu’ar annabi Habakkuk. A kan shigiyont.

[2] Ya Ubangiji, na ji irin shaharar da ka yi; na yi al’ajabi game da ayyukanka, ya Ubangiji. Ka maimaita su a kwanakinmu, ka sanar da su a lokacinmu; ka yi jinƙai ko a lokacin da kake fushi.

[3] Allah ya zo daga Teman, Mai Tsarkin nan daga Dutsen Faran. Sela Ɗaukakarsa ta rufe sammai yabonsa kuma ya cika duniya.

[4] Darajarsa ta yi kamar fitowar rana; ƙyalƙyali ya wulga daga hannunsa, inda ikonsa yake a ɓoye.

[5] Annoba ta sha gabansa; cuta kuma tana bin bayansa.

[6] Ya tsaya, ya kuwa girgiza duniya; ya duba, sai ya sa al’ummai suka yi rawan jiki. Tsofaffin duwatsu sun wargaje daɗaɗɗun tuddai kuma suka rurrushe. Hanyoyinsa dawwammamu ne.

[7] Na ga tentin Kushan cikin azaba; wuraren zaman Midiyan cikin damuwa.

[8] Ka ji haushin koguna ne, ya Ubangiji? Ko kuwa ka hasala da rafuffuka ne? Ko ka yi fushi da teku ne sa’ad da ka hau dawakanka da kuma kekunan yaƙinka masu nasara?

[9] Ka ja bakanka, ka nemi a ba ka kibiyoyi masu yawa. Sela Ka raba duniya da koguna;

[10] duwatsu sun gan ka sai suka ƙame. Ruwaye masu hauka sun yi ta fantsamawa; zurfafa suka yi ruri suka tā da raƙuman ruwansu sama.

[11] Rana da wata suka tsaya cik a sammai da ganin kibiyoyinka masu wucewa fyu, da ganin hasken māshinka mai walƙiya.

[12] Cikin hasala ka ratsa duniya cikin fushi kuma ka tattake ƙasashe.

[13] Ka fito don ka fanshi mutanenka, don ceci shafaffenka. Ka ragargaza shugaban ƙasar mugaye, ka tuɓe shi daga kai har ƙafa. Sela

[14] Da māshinsa ka soki kansa sa’ad da jarumawansa suka fito don su tarwatse mu, suna farin ciki sai ka ce masu shirin cinye matalautan da suke a ɓoye.

[15] Ka tattake teku da dawakanka, kana kaɗa manyan ruwaye.

[16] Na ji sai zuciyata ta buga, leɓunana sun yi rawa da jin murya; ƙasusuwana suka ruɓe, ƙafafuna kuma sun yi rawa. Duk da haka zan jira da haƙuri ga ranar bala’i ta zo a kan al’umman nan mai kawo mana hari.

[17] Ko da yake itace ɓaure bai tohu ba, ba kuma ’ya’ya a kuringar inabi, ko da yake zaitun bai ba da amfani ba, gonaki kuma ba su ba da abinci ba, ko da yake babu tumaki a garke, ba kuma shanu a turaku,

[18] duk da haka zan yi farin ciki da Ubangiji, zan yi murna da Allah Mai Cetona.

[19] Ubangiji Mai Iko Duka shi ne ƙarfina; yakan mai da ƙafafuna kamar na barewa, yakan sa in yi tafiya a wurare masu tsayi. Domin mai bi da kaɗe-kaɗe. A kan kayan kiɗi masu tsirkiyata.

Habakkuk — Chapters