Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:24

[1] Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.

[2] “Zan hallaka kome a fuskar duniya,” in ji Ubangiji.

[3] “Zan hallaka mutane da dabbobi; zan kuma hallaka tsuntsayen sama da kifayen teku, da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.” “Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,” in ji Ubangiji.

[4] “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda da kuma dukan mazaunan Urushalima. Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri, da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,

[5] waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki don su yi sujada ga rundunar taurari. Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji suke kuma rantsuwa da sunan Molek.

[6] Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji, ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”

[7] Ku yi shiru a gaban Ubangiji Mai Iko Duka, gama ranar Ubangiji ta yi kusa. Ubangiji ya shirya hadaya; ya kuma tsarkake waɗanda ya gayyato.

[8] “A ranar hadayar Ubangiji zan hukunta sarakuna da kuma ’ya’yan sarakuna da duk waɗanda suke sanye da rigunan ƙasashen waje.

[9] A wannan rana zan hukunta dukan waɗanda suke kauce taka madogarar ƙofa, waɗanda suke cika haikalin allolinsu da rikici da ruɗu.

[10] “A wannan rana,” in ji Ubangiji, “Za a ji kuka daga Ƙofar Kifi, kururuwa daga Sabon Mazauni, da kuma amo mai ƙarfi daga tuddai.

[11] Ku yi kururuwa, ku da kuke zaune a yankin kasuwa; za a hallaka dukan ’yan kasuwanku, dukan waɗanda suke kasuwanci da azurfa za su lalace.

[12] A wannan lokaci zan bincike Urushalima da fitilu in kuma hukunta waɗanda ba su kula ba, waɗanda suke kamar ruwan inabin da aka bar a ƙasan tukunya, waɗanda suke tsammani, ‘Ubangiji ba zai yi kome ba nagari ko mummuna.’

[13] Za a washe dukiyarsu, a rurrushe gidajensu. Za su gina gidaje amma ba za su zauna a ciki ba; za su shuka inabi amma ba za su sha ruwansa ba.”

[14] Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa, ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri. Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi, za a ji kururuwan jarumi a can.

[15] Ranan nan za tă zama ranar fushi, rana ce ta baƙin ciki da azaba, rana ce ta tashin hankali da lalacewa, ranar duhu baƙi ƙirin, ranar gizagizai da baƙin duhu,

[16] rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi gāba da birane masu mafaka, da kuma kusurwar hasumiyoyi.

[17] “Zan kawo baƙin ciki a kan mutane za su kuma yi tafiya kamar makafi, domin sun yi wa Ubangiji zunubi. Za a zubar da jininsu kamar ƙura kayan cikinsu kuma kamar najasa.

[18] Azurfarsu ko zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba a ranar fushin Ubangiji.” A cikin zafin kishinsa za a hallaka dukan duniya gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya nan da nan.

Zefaniya — Chapters