[1] Zan tsaya wurin tsarona in kuma zauna a kan katanga; zan jira in ga abin da zai ce mini, da kuma wace amsa zan bayar ga wannan kuka.
[2] Sa’an nan Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka rubuta wannan ru’uya ka bayyana ta a fili a kan alluna don mai shela yă ruga da ita, yă kai.
[3] Gama ru’uyar tana jiran ƙayyadadden lokaci; tana zancen ƙarshe kuma ba za tă zama ƙarya ba. Ko da ka ga kamar tana jinkiri, ka jira ta; lalle za tă zo, ba za tă makara ba.
[4] “Duba, abokin gāba ya cika da ɗaga kai; sha’awarsa ba daidai ba ce, amma mai adalci zai rayu ta wurin bangaskiyarsa,
[5] ba shakka, ruwan inabi ya yaudare shi; yana fariya kuma ba ya hutu. Domin shi mai haɗama ne kamar kabari kuma kamar mutuwa, ba ya ƙoshi; yakan tattara dukan al’ummai wa kansa yana kuma kama dukan mutane su zama kamammu.
[6] “Dukansu ba za su yi masa tsiya, suna yin masa ba’a da dariya ba, suna cewa, “ ‘Kaito ga wannan wanda ya tara wa kansa kayan sata ya kuma wadatar da kansa da kayan ƙwace! Har yaushe wannan abu zai ci gaba?’
[7] Masu binka bashi ba za su taso maka nan da nan ba? Ba za su farka su sa ka fargaba ba? Ta haka ka zama ganima a gare su.
[8] Domin ka washe al’ummai masu yawa, mutanen da suka rage za su washe ka. Domin ka zub da jinin mutane; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.
[9] “Kaito ga wanda ya gina masarautarsa da ƙazamar riba don yă kafa sheƙarsa can bisa, don yă tsere wa zama kango!
[10] Ka ƙulla lalacin mutane masu yawa, ta haka ka kunyatar da gidanka ka kuma hallaka ranka.
[11] Duwatsun katanga za su yi kuka, ginshiƙan katako kuma za su amsa.
[12] “Kaiton mutumin da ya gina birni da jinin da ya zubar ya kuma kafa gari ta wurin mugun aiki!
[13] Ba Ubangiji Maɗaukaki ne ya ƙudura cewa wahalar mutane ta zama mai kawai don wuta ba, cewa al’ummai su gajiyar da kansu a banza ba?
[14] Gama duniya za tă cika da sanin ɗaukakar Ubangiji, yadda ruwaye suka rufe teku.
[15] “Kaito wanda ya ba wa maƙwabtansa abin sha, yana ta zubawa daga salkan ruwan inabi har sai sun bugu, don dai yă ga tsiraicinsu.
[16] Za ka cika da kunya a maimakon ɗaukaka. Yanzu lokacinka ne! Kai ma ka sha, a kuma tone asirinka! Gama kwaf na hannun daman Ubangiji yana zuwa kewaye da kai, abin kunya kuma zai rufe darajarka.
[17] Ɓarnar da ka yi wa Lebanon zai komo kanka, kuma hallakar dabbobin da ka yi zai sa dabbobi su tsorata ka. Gama ka zub da jinin mutum; ka hallaka ƙasashe, da birane, da kuma kowa da yake cikinsu.
[18] “Ina amfanin gunki da mutum ne ya sassaƙa? Ko siffar da take koyar da ƙarya? Gama wanda ya yi shi yana dogara ne ga halittarsa; ya yi gumakan da ba sa magana.
[19] Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’ Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’ Zai iya bishewa ne? An dalaye shi da zinariya da azurfa; ba numfashi a cikinsa.”
[20] Amma Ubangiji yana a cikin haikalinsa mai tsarki; bari dukan duniya tă yi shiru a gabansa.