Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:50

[1] Kamar yadda matattun ƙudaje sukan ɓata ƙanshin turare, haka ’yar wauta takan ɓata hikima da daraja.

[2] Zuciyar mai hikima takan karkata ga yin abin da yake daidai, amma zuciyar wawa takan karkata ga yin mugun abu.

[3] Ko yayinda yake tafiya a kan hanya wawa yakan nuna cewa ba shi da hankali, yakan nuna wa kowa wawancinsa.

[4] In hankalin mai mulki ya tashi game da kai, kada ka bar inda kake, gama kwantar da hankali yakan sa a yafe manyan laifofi.

[5] Akwai muguntar da na gani a duniya, irin kuskuren da yake fitowa daga masu mulki.

[6] Akan sa wawaye a manyan matsayi, yayinda masu arziki suna ƙarƙashi.

[7] Na taɓa ganin bayi a kan dawakai, yayinda ’ya’yan sarki suna takawa a ƙasa kamar bayi.

[8] Duk wanda ya haƙa rami shi ne zai fāɗa a ciki; duk wanda ya rushe katanga, shi maciji zai sara.

[9] Duk mai farfasa duwatsu shi za su yi wa rauni; duk mai faskaren itace yana cikin hatsarinsu.

[10] In gatari ya dakushe ba a kuma wasa shi ba, dole a yi amfani da ƙarfi da yawa, amma ƙwarewa yana kawo nasara.

[11] In maciji ya sari mutum kafin a ba shi makarin gardi, ina amfanin maganin?

[12] Kalmomi daga bakin mai hikima alheri ne, amma maganganun wawa za su hallaka shi.

[13] Farkon maganarsa wauta ce, ƙarshenta kuma takan zama muguwar hauka,

[14] wawa kuma yakan yi ta surutu. Ba wanda ya san abin da zai zo wa zai iya faɗa masa abin da zai faru bayan rasuwarsa?

[15] Aikin wawa yakan gajiyar da shi, har bai san hanyar zuwa gari ba.

[16] Kaitonki, ya ke ƙasa wadda sarkinki bawa ne wadda kuma hakimanta ke ta shagali tun da safe.

[17] Mai albarka ce, ya ke ƙasa wadda sarkinki haifaffen gidan sarauta ne, wadda hakimanta suke samun abincinsu a daidai lokacin don samun ƙarfi ba don buguwa ba.

[18] In mutum rago ne, sai tsaiko yă lotsa, in hannuwansa ba masa yin kome, ɗaki yakan yi yoyo.

[19] Akan shirya abinci don jin daɗi, ruwan inabi kuwa don faranta zuciya, amma kuɗi ne amsar kome.

[20] Kada ka zagi sarki ko da a cikin tunaninka ne, ko ka zagi mai arziki ko da a ɗakin kwananka ne, gama tsuntsun sararin sama zai iya ɗauki maganarka, tsuntsu mai fikafikai zai sanar da abin da ka ce.

Mai Hadishi — Chapters