Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 2:38

[1] Ka tuna, ya Ubangiji, abin da ya faru da mu; duba, ka ga kunyar da muka sha.

[2] An ba wa baƙi gādonmu, gidajenmu kuma aka ba bare.

[3] Mun zama marayu marasa ubanni, uwayenmu kamar gwauraye.

[4] Dole mu sayi ruwan da muke sha; sai mun biya mu sami itace.

[5] Masu fafararmu sun kusa kama mu; mun gaji kuma ba dama mu huta.

[6] Mun miƙa kanmu ga Masar da Assuriya don mu sami isashen abinci.

[7] Kakanninmu sun yi zunubi kuma ba sa nan yanzu, mu ne aka bari muna shan hukuncinsu.

[8] Bayi suna mulki a kanmu, kuma ba wanda zai ’yantar da mu daga hannuwansu.

[9] Muna samun burodi a bakin rayukanmu domin takobin da yake a jeji.

[10] Fatar jikinmu ta yi zafi kamar murhu, muna jin zazzaɓi domin yunwa.

[11] An yi wa mata fyaɗe a cikin Sihiyona, da kuma budurwai a cikin garuruwan Yahuda.

[12] An rataye ’ya’yan sarakuna da hannuwansu; ba a ba wa dattawa girma.

[13] Samari suna faman yin niƙa; yara kuma suna fama da ƙyar da nauyin kayan itace.

[14] Dattawan sun bar ƙofar birnin, samari sun daina rera waƙa.

[15] Farin ciki ya rabu da zuciyarmu; rayuwarmu ta zama makoki.

[16] Rawani ya fāɗi daga kanmu. Kaiton mu gama mun yi zunubi!

[17] Domin wannan zuciyarmu ta yi sanyi; domin waɗannan abubuwa idanunmu sun dushe

[18] gama Tudun Sihiyona ya zama kufai, sai diloli ke yawo a wurin.

[19] Ya Ubangiji, kai ne mai iko har abada; kursiyinka ya dawwama cikin dukan zamani.

[20] Don mene ne kake mantawa da mu koyaushe? Me ya sa ka yashe mu da jimawa?

[21] Ka sāke jawo mu gare ka, ya Ubangiji, don mu komo; ka sabunta kwanakinmu su zama kamar yadda suke a dā

[22] sai dai in ka ƙi mu gaba ɗaya kana fushi da mu fiye da yadda za a iya aunawa.

Makoki — Chapters