[1] Ni ne mutumin da ya ga azaba ta wurin bulalar fushin Ubangiji.
[2] Ya kore ni, ya sa na yi tafiya a cikin duhu maimakon a cikin haske;
[3] ba shakka, ya juya mini baya, yana gāba da ni sau da sau, dukan yini.
[4] Ya sa fatar jikina da naman jikina sun tsufa ya kuma karya ƙasusuwana.
[5] Ya yi mini kwanton ɓauna ya kuma kewaye ni da baƙin ciki da kuma wahala.
[6] Ya sa na zauna a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu da jimawa.
[7] Ya kewaye ni yadda ba zan iya gudu ba; Ya daure ni da sarƙa mai nauyi.
[8] Ko lokacin da nake kira don neman taimako, ba ya jin addu’ata.
[9] Ya tare hanyata da tubula na duwatsu; ya sa hanyata ta karkace.
[10] Kamar beyar da take a laɓe tana jira, kamar zaki a ɓoye,
[11] ya janye ni daga kan hanya ya ɓatar da ni ya bar ni ba taimako.
[12] Ya ja kwarinsa ya sa in zama abin baratarsa.
[13] Ya harbi zuciyata da kibiyoyin kwarinsa.
[14] Na zama abin dariya ga mutanena duka; suna yi mini ba’a cikin waƙa dukan yini.
[15] Ya cika ni da kayan ɗaci ya gundure ni da abinci mai ɗaci.
[16] Ya kakkarya haƙorana da tsakuwa; ya tattake ni cikin ƙura.
[17] An hana ni salama; na manta da ko mene ne ake kira wadata.
[18] Saboda haka na ce, “Darajata ta ƙare da kuma duk abin da nake begen samu daga wurin Ubangiji.”
[19] Na tuna da azabata da kuma sintiri, da na yi ta yi da ɗacin rai.
[20] Na tuna su sosai, sai kuma na ji ba daɗi a raina.
[21] Duk da haka na tuna da wannan na kuma sa bege ga nan gaba.
[22] Domin ƙaunar Ubangiji ba mu hallaka ba; gama jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa.
[23] Sababbi ne kowace safiya; amincinka kuwa mai girma ne.
[24] Na ce wa kaina, “Ubangiji shi ne nawa; saboda haka zan jira shi.”
[25] Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;
[26] yana da kyau ka jira shiru domin samun ceton Ubangiji.
[27] Yana da kyau mutum yă sha wuya tun yana yaro.
[28] Bari yă zauna shiru shi kaɗai, gama haka Ubangiji ya sa yă yi.
[29] Bari yă ɓoye fuskarsa cikin ƙura kila akwai bege.
[30] Bari yă ba da kumatunsa a mare shi, yă kuma bari a ci masa mutunci.
[31] Gama Ubangiji ba ya yashe mutane har abada.
[32] Ko da ya kawo ɓacin rai, zai nuna tausayi sosai, ƙaunarsa tana da yawa.
[33] Gama ba haka kawai yake kawo wahala ko ɓacin rai ga ’yan adam ba.
[34] Bai yarda a tattake ’yan kurkuku a ƙasa ba,
[35] ko kuma a danne wa mutum hakkinsa a gaban Maɗaukaki,
[36] ko kuma a danne wa mutum shari’ar gaskiya ashe Ubangiji ba zai ga irin waɗannan abubuwa ba?
[37] Wane ne ya isa yă yi magana kuma ta cika in ba Ubangiji ne ya umarta ba?
[38] Ba daga bakin Maɗaukaki ne bala’i da abubuwa masu kyau suke fitowa ba?
[39] Don mene ne wani mai rai zai yi gunaguni sa’ad da aka ba shi horo domin zunubansa?
[40] Bari mu auna tafiyarmu mu gwada ta, sai mu kuma koma ga Ubangiji.
[41] Bari mu ɗaga zuciyarmu da hannuwanmu ga Allah na cikin sama, mu ce,
[42] “Mun yi zunubi mun yi tawaye ba ka kuwa gafarta ba.
[43] “Ka rufe kanka da fushi, ka fafare mu; ka karkashe mu ba tausayi.
[44] Ka rufe kanka da gajimare don kada addu’armu ta kai wurinka.
[45] Ka mai da mu tarkace da juji a cikin mutane.
[46] “Dukan maƙiyanmu suna ta yin mana magana marar daɗi.
[47] Muna cika da tsoro, da lalatarwa da hallakarwa.”
[48] Hawaye na kwararowa daga idanuna domin an hallaka mutanena.
[49] Idanuna za su ci gaba da kwararowa da hawaye, ba hutawa.
[50] Har sai in Ubangiji ya duba daga sama ya gani.
[51] Abin da nake gani yana kawo mini baƙin ciki domin dukan matan birnina.
[52] Maƙiyana suna farauta ta ba dalili kamar tsuntsu.
[53] Sun yi ƙoƙari su kashe ni a cikin rami suka kuma jajjefe ni da duwatsu;
[54] ruwaye suka rufe kaina, sai na yi tunani cewa na kusa mutuwa.
[55] Na yi kira ga sunanka, ya Ubangiji, daga rami mai zurfi.
[56] Ka ji roƙona, “Kada ka toshe kunnuwanka ka ƙi jin roƙona na neman taimako.”
[57] Ka zo kusa lokacin da na kira ka, kuma ka ce mini, “Kada ka ji tsoro.”
[58] Ya Ubangiji, ka goyi bayana; ka fanshi raina.
[59] Ya Ubangiji, ka ga inda aka yi mini ba daidai ba. Ka shari’anta, ka ba ni gaskiya!
[60] Ka ga zurfin ramakonsu, da duk mugun shirin da suke yi mini.
[61] Ya Ubangiji, ka ji zaginsu, da duka mugun shirin da suke yi mini
[62] Abin da maƙiyana suke yin raɗa a kai game da ni duk yini.
[63] Dube su! A zaune ko a tsaye, suna yi mini ba’a cikin waƙoƙinsu.
[64] Ka ba su abin da ya dace su samu, ya Ubangiji, domin abin da hannuwansu suka yi.
[65] Ka sa yana ta rufe zuciyarsu, kuma bari la’anarka ta bi su.
[66] Ka fafare su cikin fushi ka hallaka su daga cikin duniya ta Ubangiji.