[1] Musa tare da dattawan Isra’ila suka umarci mutane suka ce, “Ku kiyaye dukan umarnai da na ba ku a yau.
[2] Sa’ad da kuka haye Urdun zuwa cikin ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ku kakkafa waɗansu manyan duwatsu, ku yi musu shafe da farar ƙasa.
[3] Ku rubuta dukan waɗannan kalmomin doka a kansu, sa’ad da kuka haye kuka shiga ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, ƙasa mai zub da madara da zuma, kamar dai yadda Ubangiji Allah na kakanninku, ya yi muku alkawari.
[4] Sa’ad da kuma kuka haye Urdun, ku kakkafa waɗannan duwatsu a bisa Dutsen Ebal, kamar yadda na umarce a yau, ku yi musu shafe da farar ƙasa.
[5] Ku gina bagade wa Ubangiji Allahnku, bagaden dutse. Kada ku yi amfani da wani kayan aiki na ƙarfe a kansu.
[6] Ku gina bagaden Ubangiji Allahnku da duwatsun fili, ku kuma miƙa hadaya ta ƙonawa a kansa ga Ubangiji Allahnku.
[7] Ku miƙa hadayun salama a can, kuna ci, kuna farin ciki a gaban Ubangiji Allahnku.
[8] Za ku kuma rubuta a fayyace dukan kalmomin wannan doka a kan waɗannan duwatsun da kuka kakkafa.”
[9] Sai Musa da firistoci waɗanda suke Lawiyawa suka ce wa dukan Isra’ila, “Ku yi shiru, ya Isra’ila, ku saurara! Yanzu kun zama mutanen Ubangiji Allahnku.
[10] Ku yi biyayya ga Ubangiji Allahnku, ku bi umarnansa da ƙa’idodin da nake ba ku a yau.”
[11] A wannan rana Musa ya umarce mutane,
[12] Sa’ad da kuka haye Urdun, sai waɗannan kabilai su tsaya a bisa Dutsen Gerizim su sa wa jama’a albarka, wato, kabilar Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar, Yusuf da Benyamin.
[13] Waɗannan kabilai kuma za su tsaya a bisa Dutsen Ebal su furta la’ana, wato, kabilar Ruben, Gad, Asher, Zebulun, Dan da Naftali.
[14] Lawiyawa za su karanta wa dukan mutanen Isra’ila da babbar murya su ce,
[15] “La’ananne ne mutumin da ya sassaƙa siffa, ko ya yi zubin gunki, abar ƙyama ce ga Ubangiji, aikin hannu mai sana’a da aka kafa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[16] “La’ananne ne mutumin da ya ƙasƙantar da mahaifinsa ko mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[17] “La’ananne ne mutumin da ya gusar da dutsen da aka kafa don nuna shaidar iyaka.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[18] “La’ananne ne mutumin da ya karkatar da makaho daga hanya.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[19] “La’ananne ne mutumin da ya yi rashin adalci ga baƙo, maraya ko gwauruwa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[20] “La’ananne ne mutumin da ya kwana da matar mahaifinsa, gama ya ƙasƙantar da gadon mahaifinsa ke nan.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[21] “La’ananne ne mutumin da ya yi jima’i da dabba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[22] “La’ananne ne mutumin da ya kwana da ’yar’uwarsa, ’yar mahaifinsa ko ’yar mahaifiyarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[23] “La’ananne ne mutumin da ya kwana da mahaifiyar matarsa.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[24] “La’ananne ne mutumin da ya kashe maƙwabcinsa a ɓoye.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[25] “La’ananne ne mutumin da ya karɓi cin hanci don yă kashe marar laifi.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”
[26] “La’ananne ne mutumin da bai yi na’am da kalmomin wannan doka ta wurin aikata su ba.” Sai dukan mutane su ce, “Amin!”