Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:17

[1] A lokacin Ubangiji ya ce mini, “Ka sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, ka haura wurina a kan dutse. Ka kuma yi akwatin katako.

[2] Ni kuwa zan yi rubutu a kan allunan nan biyu, kalmomin da suke a alluna na farko, waɗanda ka farfashe. Za a ajiye su a cikin akwatin.”

[3] Sai na yi akwatin da itacen ƙirya, na kuma sassaƙa alluna biyu na dutse kamar na farko, sai na haura dutse da alluna biyun a hannuwana.

[4] Ubangiji kuwa ya sāke yin rubutu a waɗannan alluna abin da ya rubuta a allunan farko, wato, Dokoki Goma da ya furta a kan dutse a tsakiyar wuta, a ranar da mutane suka taru. Sai Ubangiji ya ba ni su.

[5] Sa’an nan na sauko daga dutsen, na kuma ajiye allunan a cikin akwatin da na yi, yadda Ubangiji ya umarce ni, kuma suna can a yanzu.

[6] (Isra’ilawa suka kama hanya daga rijiyoyin Beyerot Bene Ya’akan zuwa Mosera. A can Haruna ya rasu, aka kuma binne shi. Sai Eleyazar ɗansa ya gāje shi a matsayin firist.

[7] Daga can suka tashi zuwa Gudgoda, daga Gudgoda kuma suka tafi Yotbata, ƙasa mai rafuffukan ruwa.

[8] A lokacin Ubangiji ya keɓe kabilar Lawi don su riƙa ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, su tsaya a gaban Ubangiji, su riƙa yin masa hidima, su kuma sa albarka a cikin sunansa, yadda suke yi har wa yau.

[9] Shi ya sa Lawiyawa ba su da rabo, ko gādo a cikin ’yan’uwansu; Ubangiji ne gādonsu yadda Ubangiji Allahnku ya faɗa musu.)

[10] To, na kasance a kan dutse yini arba’in da dare arba’in kamar yadda dā na yi da farko. Ubangiji kuwa ya saurare ni a wannan lokaci kuma. Ba nufinsa ba ne yă hallaka ku.

[11] Ubangiji ya ce mini, “Ka sauka, ka jagoranci mutanen a hanyarsu, domin su shiga, su kuma mallaki ƙasar da na rantse wa kakanninsu, zan ba su.”

[12] Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku,

[13] ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?

[14] Sammai, har da sama sammai, da duniya, da kome da yake cikinta na Ubangiji Allahnku ne.

[15] Duk da haka Ubangiji ya ƙaunaci kakanninku, ya kuma zaɓe ku, ku zuriyarsu, a bisa dukan al’ummai, yadda yake a yau.

[16] Saboda haka sai ku kame zukatanku, kada ku ƙara yin taurinkai.

[17] Gama Ubangiji Allahnku ne Allahn alloli da Ubangijin iyayengiji, Allah mai girma, mai ƙarfi da kuma mai banrazana, wanda ba ya sonkai, ba ya cin hanci.

[18] Yakan tsare marayu da gwauraye, yana ƙaunar baƙon da yake zama a cikinku, yana ba su abinci da tufafi.

[19] Sai ku ƙaunaci baƙi, gama dā ku ma baƙi ne a ƙasar Masar.

[20] Ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku kuma bauta masa. Ku manne masa, ku kuma yi rantsuwarku da sunansa.

[21] Shi ne abin yabonku; shi ne Allahnku, wanda ya aikata muku waɗancan manya abubuwa banmamaki masu banrazanar da kuka gani da idanunku.

[22] Kakanninku da suka gangara zuwa Masar, su saba’in ne, yanzu kuwa Ubangiji Allahnku ya sa kuka ƙaru, kuka zama kamar taurari a sama.

Maimaitawar Shari’a — Chapters