Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 5:07

[1] Sai na ji wata babbar murya daga haikalin tana ce wa mala’iku bakwai nan, “Ku tafi ku zuba kwanoni bakwai nan na fushin Allah a kan duniya.”

[2] Mala’ika na fari ya je ya juye kwanonsa a bisan ƙasa, sai munanan gyambuna masu zafi suka fito a jikin mutanen da suke da alamar dabbar suka kuma yi wa siffarta sujada.

[3] Mala’ika na biyu ya juye kwanonsa a bisan teku, sai tekun ya zama jini kamar na mataccen mutum, kuma kowane abu mai rai da yake cikin tekun ya mutu.

[4] Mala’ika na uku ya juye kwanonsa a bisan koguna da maɓulɓulan ruwa, sai suka zama jini.

[5] Sa’an nan na ji mala’ikan da yake lura da ruwaye ya ce, “Kai mai adalci ne cikin waɗannan hukuntai, kai da kake yanzu, kake kuma a dā, Mai Tsarki, saboda yadda ka yi hukuncin nan;

[6] gama sun zub da jinin tsarkakanka da kuma annabawanka, ka kuwa ba su jini su sha, yadda ya dace da su.”

[7] Na kuma ji bagaden ya amsa, “I, Ubangiji Allah, Maɗaukaki, hukuntanka daidai yake na adalci ne kuma.”

[8] Mala’ika na huɗu ya juye kwanonsa a bisan rana, sai aka ba wa rana iko ta ƙona mutane da wuta.

[9] Aka ƙone su da zafin wuta mai tsanani suka kuwa la’anci sunan Allah wanda yake da iko a kan waɗannan annoban, amma suka ƙi su tuba su kuma ɗaukaka shi.

[10] Mala’ika na biyar ya juye kwanonsa a bisan gadon sarautar dabbar, mulkinta kuwa ya zama duhu. Mutane suka yi ta cizon bakinsu saboda azaba

[11] suka kuma la’anci Allah na sama saboda zafinsu, da kuma saboda gyambunansu, amma suka ƙi su tuba daga abin da suka riga suka yi.

[12] Mala’ika na shida ya juye kwanonsa a bisan babban kogin Yuferites, sai ruwansa ya shanye don a shirya hanya saboda sarakuna daga Gabas.

[13] Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan.

[14] Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.

[15] “Ga shi, ina zuwa kamar ɓarawo! Mai albarka ne wanda yake zama a faɗake yana kuma saye da tufafinsa, don kada yă yi tafiya tsirara a kuma kunyata shi.”

[16] Sa’an nan aka tattara sarakuna zuwa wurin da a Ibraniyanci ake kira Armageddon.

[17] Mala’ika na bakwai ya juye kwanonsa cikin iska, daga haikalin kuwa sai aka ji wata babbar murya daga kursiyin, tana cewa, “An gama!”

[18] Sai ga walƙiya, ƙararraki, tsawa da kuma matsananciyar girgizar ƙasa. Ba a taɓa yin irin wannan girgizar ƙasar ba, tun kasancewar mutum a duniya, girgizar ƙasar kuwa gawurtacciya ce.

[19] Babban birnin ya rabu kashi uku, biranen al’ummai kuma suka rurrushe. Allah ya tuna da Babilon Mai Girma ya kuma ba ta kwaf cike da ruwan inabin fushinsa.

[20] Kowane tsibiri ya gudu ba a kuwa ƙara ganin duwatsu ba.

[21] Daga sararin sama manyan ƙanƙara masu nauyin gaske suka fāɗo a kan mutane. Suka kuma la’anci Allah saboda annobar ƙanƙarar, domin annobar ta yi muni ƙwarai.

Ru’uya ta Yohanna — Chapters