Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:16

[1] Bulus, ɗan kurkuku saboda Kiristi Yesu, da kuma Timoti ɗan’uwanmu, Zuwa ga Filemon ƙaunataccen abokinmu da kuma abokin aikinmu,

[2] zuwa kuma ga Affiya ’yar’uwarmu, zuwa kuma ga Arkiffus abokin famarmu, da zuwa kuma ga ikkilisiyar da take taruwa a gidanka.

[3] Alheri da salama daga Allah Ubanmu da kuma Ubangiji Yesu Kiristi, su kasance tare da ku.

[4] Kullum nakan gode wa Allahna sa’ad da nake tuna da kai cikin addu’o’ina,

[5] domin ina jin labari bangaskiyarka cikin Ubangiji Yesu da kuma ƙaunarka da kake yi saboda dukan tsarkaka.

[6] Ina addu’a ka zama mai ƙwazo cikin shaida bangaskiyarka, domin ka sami cikakken fahimta ta kowane abin da yake nagarin da muke da shi cikin Kiristi.

[7] Ƙaunarka ta sa ni farin ciki ƙwarai ta kuma ƙarfafa ni, domin kai, ɗan’uwa, ka wartsake zukatan tsarkaka.

[8] Saboda haka, ko da yake cikin Kiristi ina iya yin ƙarfin hali in umarce ka ka yi abin da ya kamata,

[9] duk da haka ina roƙonka saboda ƙauna, na fi so in roƙe ka, ni Bulus tsoho, a yanzu kuma ga ni ɗan sarƙa saboda Kiristi Yesu.

[10] Ina roƙonka saboda ɗana Onesimus, wanda ya zama ɗana yayinda nake cikin sarƙoƙi.

[11] Dā kam, ba shi da amfani a gare ka, amma yanzu ya zama da amfani a gare ka da kuma gare ni.

[12] Ina aike shi yă koma gare ka, shi da yake zuciyata.

[13] Na so in riƙe shi a wurina a madadinka domin yă taimake ni yayinda nake cikin sarƙoƙi saboda bishara.

[14] Sai dai ban so in yi kome ban da yardarka ba, domin kowane alherin da za ka yi, yă fito daga zuciyarka, ba na tilas ba.

[15] Wataƙila abin da ya sa aka raba ka da shi na ɗan lokaci ƙanƙani shi ne don ka same shi da amfani

[16] ba kamar bawa kuma ba, sai dai fiye da bawa, a matsayin ƙaunataccen ɗan’uwa. Shi ƙaunatacce ne sosai a gare ni amma a gare ka ya ma fi zama ƙaunatacce, kamar mutum da kuma kamar ɗan’uwa a cikin Ubangiji.

[17] Saboda haka in ka ɗauke ni a kan ni abokin tarayya ne, sai ka marabce shi kamar yadda za ka marabce ni.

[18] In ya yi maka wani laifi ko kuma yana riƙe maka wani bashi, sai ka mai da shi a kaina.

[19] Ni, Bulus, nake rubuta wannan da hannuna. Zan biya ka, kada ma a yi zancen ranka da kake riƙe mini bashi.

[20] Ina fata, ɗan’uwa, zan sami amfani daga gare ka cikin Ubangiji; ka wartsake zuciyata cikin Kiristi.

[21] Da tabbacin biyayyarka, ina rubuta maka, da sanin za ka yi fiye da abin da na ce.

[22] Abu guda ya rage, ka shirya mini masauƙi, domin ina bege za a mayar da ni gare ku albarkacin addu’o’inku.

[23] Efafaras, abokin tarayyata a kurkuku cikin Kiristi Yesu, yana gaishe ka.

[24] Haka kuma Markus, Aristarkus, Demas da kuma Luka, abokan aikina.

[25] Alherin Ubangiji Yesu Kiristi yă kasance da ruhunku.