Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:44

[1] Eliyashib babban firist da ’yan’uwansa firistoci suka tashi suka sāke gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa ƙofofinta a wurarensu, suka yi ginin har Hasumiyar Ɗari, wadda suka tsarkake, da kuma Hasumiyar Hananel.

[2] Mutanen Yeriko kuwa suka kama ginin daga mahaɗin, Zakkur ɗan Imri kuma ya fara ginin biye da su.

[3] ’Ya’yan Hassenaya ne suka gina Ƙofar Kifi. Suka kafa ginshiƙan, suka kuma sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu.

[4] Kusa da su kuma, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz ne ya yi gyare-gyaren. Biye da shi kuma sai Meshullam ɗan Berekiya, ɗan Meshezabel ya yi gyare-gyare. Kusa da shi Zadok ɗan Ba’ana shi ma ya yi gyare-gyare.

[5] Mutanen Tekowa ne suka yi gyare-gyare biye da shi, amma manyan garinsu suka ƙi su sa hannu cikin aikin da shugabanninsu suka bayar.

[6] Yohiyada ɗan Faseya, da Meshullam ɗan Besodehiya ne suka gyara Ƙofar Yeshana. Suka kafa katakanta, suka sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta.

[7] Biye da su, mutanen Gibeyon da Mizfa Melatiya na Gibeyon da Yadon Meronot waɗanda suke ƙarƙashin ikon gwamnan Kewayen Kogin Yuferites ne suka yi gyare-gyaren.

[8] Uzziyel ɗan Harhahiya, ɗaya daga cikin masu ƙeran zinariya ne ya yi gyare-gyaren sashe na biye; sai Hananiya, ɗaya daga cikin masu yin turare, ya yi gyare-gyaren biye da wannan. Suka gyara Urushalima har zuwa Katanga Mai Faɗi.

[9] Refahiya ɗan Hur, mai mulkin rabin yankin Urushalima, ya yi gyare-gyaren sashe na biye.

[10] Kusa da Refahiya, Yedahiya ɗan Harumaf ya yi gyare-gyaren daga gaban gidansa, sai Hattush ɗan Hashabnehiya ya yi gyare-gyaren biye da shi.

[11] Malkiya ɗan Harim, da Hasshub ɗan Fahat-Mowab ya yi gyare-gyaren wani sashe da kuma Hasumiyar Wurin Gashi.

[12] Shallum ɗan Hallohesh, mai mulkin ɗayan rabin yankin Urushalima ya yi gyare-gyaren sashe na biye tare da taimakon ’ya’yansa mata.

[13] Hanun da mazaunan Zanowa ne suka gyara Ƙofar Kwari. Suka sāke gina ta suka sa ƙofofinta, da sakatunta, da sandunan ƙarfenta a wurarensu. Suka kuma gyara yadi ɗari biyar na katangar har zuwa Ƙofar Juji.

[14] Malkiya ɗan Rekab mai mulkin yankin Bet-Hakkerem ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Juji. Ya sāke gina ta ya kuma sa sakatunta, da sanduna ƙarfenta a wurarensu.

[15] Shallum ɗan Kol-Hoze mai mulkin Mizfa ne ya yi gyare-gyaren Ƙofar Maɓuɓɓuga. Ya sāke gina ta, ya yi mata jinƙa yana sa ƙofofinta, da sakatunta, da kuma sandunan ƙarfenta a wurarensu. Ya kuma gyara katangar tafkin Silowam, ta Lambun Sarki, har zuwa matakalan da suka gangara daga Birnin Dawuda.

[16] Gaba da shi, Nehemiya ɗan Azbuk, mai mulkin rabin yankin Bet-Zur ne ya yi gyare-gyaren har zuwa kusa da kaburburan Dawuda, har zuwa haƙaƙƙen tafki da kuma Gidan Jarumawa.

[17] Biye da shi, Lawiyawa a ƙarƙashin Rehum ɗan Bani ne suka yi gyare-gyaren. Kusa da su, Hashabiya mai mulkin rabin yankin Keyila ne ya yi gyare-gyaren don yankinsa.

[18] Biye da shi, ’yan’uwansu Lawiyawa ne a ƙarƙashin Binnuyi ɗan Henadad, mai mulkin ɗayan rabin yankin Keyila suka yi gyare-gyaren.

[19] Biye da su, Ezer ɗan Yeshuwa, mai mulkin Mizfa, ya yi gyara wani sashe, daga inda yake fuskantar hawan gidan makamai har zuwa kusurwa.

[20] Biye da shi, Baruk ɗan Zakkai da ƙwazo ya gyara wani sashe, daga kusurwa zuwa mashigin gidan Eliyashib babban firist.

[21] Biye da shi, Meremot ɗan Uriya, ɗan Hakkoz, ya yi gyaran wani sashe, daga mashigin gidan Eliyashib zuwa ƙarshensa.

[22] Firistoci daga kewayen yankin ne suka yi gyare-gyaren biye da shi.

[23] Can gaba da su, Benyamin da Hasshub ne suka yi gyare-gyaren a gaban gidansu, biye da su kuwa, Azariya ɗan Ma’asehiya, ɗan Ananiya ne ya yi gyare-gyaren kusa da gidansa.

[24] Biye da shi, Binnuyi ɗan Henadad ya yi gyaran wani sashe, daga gidan Azariya zuwa kusurwa,

[25] sai Falal ɗan Uzai ya yi aiki ɗaura da kusurwa da kuma doguwar hasumiya daga fadar da take bisa kusa da shirayin masu tsaro. Biye da shi, Fedahiya ɗan Farosh

[26] da masu hidimar haikali da suke zama a tudun Ofel ne suka yi gyare-gyaren har zuwa wani wuri ɗaura da Ƙofar Ruwa wajen gabas da kuma doguwar hasumiya.

[27] Biye da su, mutanen Tekowa suka yi gyaran wani sashe, daga babbar doguwar hasumiya zuwa katangar Ofel.

[28] Daga Ƙofar Doki, firistoci ne suka yi gyare-gyaren, kowanne a gaban gidansa.

[29] Biye da su, Zadok ɗan Immer ya yi gyare-gyaren ɗaura da gidansa. Biye da shi, Shemahiya ɗan Shekaniya, mai tsaron Ƙofar Gabas ya yi gyare-gyare.

[30] Biye da shi, Hananiya ɗan Shelemiya, da Hanun, ɗa na shida na Zalaf, suka gyara wani sashe. Biye da su, Meshullam ɗan Berekiya ya yi gyare-gyaren ɗaura da wurin zamansa.

[31] Biye da shi, Malkiya, ɗaya daga cikin masu ƙera zinariya ya yi gyare-gyaren har zuwa gidan masu hidimar haikali da kuma ’yan kasuwa, ɗaura da Ƙofar Bincike, har zuwa ɗakin da yake bisa kusurwar.

[32] Maƙeran zinariya da ’yan kasuwa suka gyara wani sashi tsakanin ɗakin da yake bisa kusurwa da Ƙofar Tumaki.

Nehemiya — Chapters