[1] Mai hari yana matsowa a kanki, Ninebe. Ki tsare mafaka, ki yi gadin hanya ki sha ɗamara ki tattaro dukan ƙarfinki!
[2] Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub, kamar ta Isra’ila, ko da yake masu washewa sun washe su suka kuma lalatar da inabinsu.
[3] Garkuwoyin sojojinsa ja wur ne; jarumawansa suna sanye da kaya masu ruwan jan garura. Ƙarafan kekunan yaƙi suna walƙiya a ranar da aka shirya su; ana kaɗa māsu da bantsoro.
[4] Kekunan yaƙi sun zabura a tituna, suna kai da kawowa a dandali. Suna walƙiya kamar tocila suna sheƙawa a guje kamar walƙiya.
[5] Ninebe ta tattara rundunarta, duk da haka sun yi ta tuntuɓe a kan hanyarsu. Sun ruga zuwa katangan birnin, sun sanya garkuwar kāriya a inda ya kamata.
[6] An buɗe ƙofofin rafuffukan sai wurin ya rurrushe.
[7] An umarta cewa birnin za tă tafi bauta, za a kuma yi gaba da su. Bayi ’yan mata suna kuka kamar tattabaru suna buga ƙirjinsu.
[8] Ninebe tana kama da tafki, wanda ruwanta yana yoyo. Suna kuka suna cewa, “Ku tsaya! Ku tsaya,” amma ba wanda ya waiga.
[9] A washe azurfa; a washe zinariya; dukiyarsu ba ta da iyaka, arzikinsu kuma ba ya ƙarewa.
[10] Ta zama wofi, an washe ta, an tuɓe ta! Zukata sun narke, gwiwoyi suna kaɗuwa, jikuna suna rawa, fuskoki duk sun kwantsare!
[11] Ina kogon zakokin nan yake yanzu, inda suka ciyar da ’ya’yansu, inda zaki da zakanya sukan shiga, da ’ya’yansu, ba mai damunsu
[12] Zaki ya kashe abin da ya ishe ’ya’yansa ya kuma murɗe wuyan dabbobi ya cika wurin zamansa da abin da ya kama ya cika kogwanninsa da abin da ya kashe.
[13] “Ina gāba da ke,” in ji Ubangiji Maɗaukaki. “Zan ƙone kekunan yaƙinki, takobi kuma zai fafare ’ya’yan zakokinki. Ba kuma zan bar miki namun jejin da za ki kashe a duniya ba. Ba kuwa za a ƙara jin muryar ’yan saƙonki ba.”