Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:52

[1] Yesu ya shiga jirgin ruwa, ya ƙetare ya zo garinsa.

[2] Waɗansu mutane suka kawo masa wani shanyayye, kwance a tabarma. Da Yesu ya ga bangaskiyarsu, sai ya ce wa shanyayyen, “Kada ka damu saurayi, an gafarta maka zunubanka.”

[3] Da jin wannan, waɗansu malaman dokoki suka ce wa juna, “Wannan mutum yana yin saɓo!”

[4] Sane da tunaninsu, Yesu ya ce, “Me ya sa kuke da mugun tunani a zuciyarku?

[5] Wanne ya fi sauƙi, a ce, ‘An gafarta maka zunubanka,’ ko kuwa a ce, ‘Tashi ka yi tafiya?’

[6] Amma don ku san cewa Ɗan Mutum yana da iko a duniya yă gafarta zunubai.” Sai ya ce wa shanyayyen, “Tashi, ɗauki tabarmarka ka tafi gida.”

[7] Mutumin kuwa ya tashi ya tafi gida.

[8] Da taron suka ga haka, sai suka cika da tsoro, suka yabi Allah wanda ya ba wa mutane irin ikon nan.

[9] Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

[10] Yayinda Yesu yake cin abinci a gidan Mattiyu, masu karɓar haraji da yawa da kuma masu zunubi suka zo suka kuwa ci tare da shi da kuma almajiransa.

[11] Sa’ad da Farisiyawa suka ga haka, sai suka tambayi almajiransa suka ce, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji, da masu zunubi?”

[12] Da jin wannan, Yesu ya ce, “Ai, ba masu lafiya ba ne su bukatar likita, sai dai marasa lafiya.

[13] Amma ku je ku koyi abin da wannan yake nufi, ‘Jinƙai nake bukata, ba hadaya ba.’ Gama ban zo domin in kira masu adalci ba, sai dai masu zunubi.”

[14] Sai almajiran Yohanna suka zo suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa mu da Farisiyawa muke azumi, amma almajiranka ba sa yi?”

[15] Yesu ya amsa ya ce, “Yaya baƙin ango za su yi makoki yayinda yake tare da su? Lokaci yana zuwa da za a ɗauke ango daga gare su, sa’an nan za su yi azumi.

[16] “Ba mai yin faci da sabon ƙyalle a kan tsohuwar riga, gama facin zai kece rigar yă sa kecewar ma ta fi ta dā muni.

[17] Mutane kuma ba sa zuba sabon ruwan inabi a cikin tsofaffin salkuna. In suka yi haka, salkunan za su farfashe, ruwan inabin kuwa yă zube salkunan kuma su lalace. A’a, ai, sukan zuba sabon ruwan inabi ne a cikin sababbin salkuna, don a kiyaye dukan biyun.”

[18] Yayinda yake faɗin wannan, sai wani mai mulki ya zo ya durƙusa a gabansa ya ce, “Yanzu-yanzu diyata ta rasu. Amma ka zo ka ɗibiya hannunka a kanta, za tă kuwa rayu.”

[19] Yesu ya tashi ya tafi tare da shi, haka ma almajiransa.

[20] A daidai wannan lokaci sai ga wata mace wadda ta yi shekaru goma sha biyu tana zub da jini ta raɓo ta bayansa ta taɓa gefen rigarsa.

[21] Ta ce a ranta, “Ko da rigarsa ce kawai na taɓo, zan warke.”

[22] Yesu ya juya ya gan ta. Sai ya ce, “Kada ki damu diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke.” Nan take macen ta warke.

[23] Da Yesu ya shiga gidan mai mulkin ya ga masu busan sarewa da taro mai hayaniya,

[24] sai ya ce, “Ku ba da wuri. Ai, yarinyar ba tă mutu ba, tana barci ne.” Amma suka yi masa dariya.

[25] Bayan an fitar da taron waje, sai ya shiga ciki ya kama yarinyar a hannu, ta kuwa tashi.

[26] Labarin wannan kuwa ya bazu ko’ina a yankin.

[27] Da Yesu ya fita daga can, sai waɗansu makafi biyu suka bi shi, suna kira, suna cewa, “Ka yi mana jinƙai, Ɗan Dawuda!”

[28] Da ya shiga cikin gida, sai makafin nan suka zo wurinsa, ya kuma tambaye su, “Kun gaskata cewa ina iya yin wannan?” Suka amsa suka ce, “I, Ubangiji.”

[29] Sa’an nan ya taɓa idanunsu ya ce, “Bisa ga bangaskiyarku a yi muku haka”;

[30] sai idanunsu suka buɗe. Yesu ya gargaɗe su sosai ya ce, “Ku lura kada wani yă san wani abu game da wannan.”

[31] Amma suka fita suka yi ta baza labari game da shi ko’ina a wannan yankin.

[32] Yayinda suke fitowa, sai aka kawo wa Yesu wani mutum mai aljani, da ba ya iya magana.

[33] Sa’ad da aka fitar da aljanin kuwa, sai beben ya yi magana. Taron suka yi mamaki suka ce, “Ba a taɓa ganin irin wannan abu a Isra’ila ba.”

[34] Amma Farisiyawa suka ce, “Ai, da ikon sarkin aljanu yake fitar da aljanu.”

[35] Yesu ya zazzaga dukan garuruwa da ƙauyuka, yana koyarwa a majami’unsu, yana wa’azin labari mai daɗi na mulkin yana kuma warkar da kowace irin cuta da rashin lafiya.

[36] Da ya ga taron mutane, sai ya ji tausayinsu, domin an wulaƙanta su ba su kuma da mai taimako, kamar tumaki marasa makiyayi.

[37] Sai ya ce wa almajiransa, “Girbi yana da yawa, amma ma’aikata kaɗan ne.

[38] Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi, yă aiko da ma’aikata cikin gonarsa na girbi.”

Mattiyu — Chapters