Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:41

[1] To, a lokacin, sai shugabannin iyalan Lawiyawa suka je wurin Eleyazar firist, Yoshuwa ɗan Nun da kuma shugabannin sauran iyalan kabilu na Isra’ila a

[2] Shilo cikin Kan’ana, suka ce musu, “Ubangiji ya yi umarni ta wurin Musa cewa a ba mu garuruwan da za mu zauna a ciki, da wurin kiwo mai kyau don dabbobinmu.”

[3] Saboda haka kamar yadda Ubangiji ya umarta, sai Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo daga cikin gādonsu.

[4] Ƙuri’a ta farko ta fāɗa a kan Kohatawa bisa ga iyalansu. Sai aka ba wa Lawiyawa waɗanda suke ’yan zuriyar Haruna, firist, garuruwa goma sha uku daga kabilan Yahuda, Simeyon da Benyamin.

[5] Sauran Kohatawan kuma aka ba su garuruwa goma daga iyalan kabilar Efraim, Dan da kuma rabi kabilar Manasse.

[6] Aka kuma ba wa zuriyar Gershon garuruwa goma sha uku daga iyalan kabilan Issakar, Asher, Naftali, da kuma rabin kabilar Manasse a Bashan.

[7] Aka ba wa zuriyar Merari bisa ga iyalansu, garuruwa goma sha biyu daga kabilan Ruben, Gad da Zebulun.

[8] Haka Isra’ilawa suka ba wa Lawiyawa waɗannan garuruwa da wuraren kiwo masu kyau, yadda Ubangiji ya umarta ta wurin Musa.

[9] Daga kabilan Yahuda da Simeyon ne aka ba su waɗannan garuruwan da aka ambata,

[10] (ga garuruwan da aka ba wa zuriyar Haruna waɗanda suke daga iyalan Kohatawa na Lawiyawa, domin ƙuri’a ta farko ta fāɗa a kansu),

[11] an ba su, Kiriyat Arba (wato, Hebron), da wurin kiwon da yake kewaye da ƙasar kan tudu ta Yahuda. (Arba shi ne kakan Anak.)

[12] Amma sai aka ba Kaleb ɗan Yefunne filayen da kuma ƙauyukan da suke kewaye da birnin, su zama nasa.

[13] Sai aka ba zuriyar Haruna firist, ƙasar Hebron (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Libna,

[14] da Yattir, da Eshtemowa,

[15] da Holon, da Debir,

[16] da Ayin, da Yutta, da kuma Bet-Shemesh, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa tara ke nan daga kabilun nan biyu, Yahuda da Simeyon.

[17] Daga kabilar Benyamin kuwa aka ba su, Gibeyon, Geba,

[18] Anatot da Almon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.

[19] Duka-duka garuruwan firistoci, zuriyar Haruna, su goma sha uku ne tare da wuraren kiwonsu.

[20] Aka kuma ba wa sauran Kohatawa, iyalan Lawiyawa, garuruwa daga kabilar Efraim.

[21] A ƙasar kan tudu ta Efraim, aka ba su, Shekem (garin masu neman mafaka don sun yi kisa) da Gezer,

[22] Kibzayim da Bet-Horon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.

[23] Haka kuma daga kabilar Dan, aka ba su, Elteke, Gibbeton,

[24] Aiyalon da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.

[25] Daga rabin kabilar Manasse kuwa aka ba su, Ta’anak da Gat-Rimmon, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan.

[26] Dukan garuruwan nan goma tare da wuraren kiwonsu ne aka ba sauran iyalan Kohatawa.

[27] Aka ba wa zuriyar Gershon, waɗanda suke Lawiyawa, rabo. Daga rabin kabilar Manasse, Golan a cikin Bashan (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), da Be’eshtera, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa biyu ke nan;

[28] daga kabilar Issakar kuma aka ba su Kishiyon, Daberat,

[29] Yarmut da En Gannim, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;

[30] daga kabilar Asher kuwa aka ba su, Mishal, Abdon,

[31] Helkat da Rehob, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;

[32] daga kabilar Naftali kuma aka ba su, Kedesh a cikin Galili (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Hammon-Dor da kuma Kartan, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa uku ke nan.

[33] Duka-duka, garuruwan iyalan Gershonawa goma sha uku ne, tare da wuraren kiwonsu.

[34] Aka ba wa iyalan Merari (sauran Lawiyawa) garuruwa, daga kabilar Zebulun, wato, Yokneyam, Karta,

[35] Dimna da kuma Nahalal, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;

[36] daga kabilar Ruben kuma aka ba su, Bezer, Yahza,

[37] Kedemot da kuma Mefa’at, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan;

[38] daga kabilar Gad kuwa aka ba su, Ramot Gileyad (garin masu neman mafaka don sun yi kisa), Mahanayim,

[39] Heshbon da kuma Yazer, tare da wuraren kiwonsu, garuruwa huɗu ke nan.

[40] Duka-duka garuruwan da aka ba iyalan mutanen Merari, waɗanda su ne sauran Lawiyawa, garuruwa goma sha biyu ne.

[41] Jimillar birane da wurarensu na kiwon da aka ba Lawiyawa daga cikin mallakar jama’ar Isra’ila guda arba’in da takwas ne.

[42] Dukan garuruwan nan kowannensu yana kewaye da wurin kiwo.

[43] Ubangiji kuwa ya ba Isra’ilawa dukan ƙasar da ya yi wa kakanninsu alkawari, suka kuwa mallake ta, suka zauna a cikinta.

[44] Ubangiji ya ba su hutawa a kowane gefe kamar yadda ya yi wa kakanninsu alkawari, ba ko ɗaya daga cikin abokan gābansu da ya iya cinsu da yaƙi.

[45] Ubangiji kuwa ya cika kowane alkawarin alherin da ya yi wa mutanen Isra’ila.

Yoshuwa — Chapters