[1] Sa’an nan sai maganar Ubangiji ta zo wa Yunana sau na biyu.
[2] “Tafi babban birnin nan Ninebe, ka yi masa shelar saƙon da na ba ka.”
[3] Sai Yunana ya yi biyayya da maganar Ubangiji, ya tafi Ninebe. Ninebe birni ne da yake da muhimmanci, wanda sai an ɗauki kwana uku kafin a iya zaga shi.
[4] A rana ta fari, Yunana ya kama tafiya yana ratsa birnin. Sai ya yi shela cewa, “Nan da kwana arba’in za a hallaka Ninebe?”
[5] Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki.
[6] Da saƙon Yunana ya kai kunnen sarkin Ninebe, sai ya tashi daga kujerar mulkinsa, ya tuɓe alkyabbarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.
[7] Sai ya yi umarni a Ninebe cewa, “Bisa ga umarnin sarki da fadawansa. “Kada a bar wani mutum ko dabba, garke ko shannu, su ɗanɗana wani abu; kada a bari su ci ko su sha.
[8] Bari kowane mutum da dabba yă yafa rigunan makoki. Kowa yă roƙi Allah da gaske, kowa kuma yă bar mugayen ayyukan da yake yi.
[9] Wa ya sani? Ko Allah zai ji tausayinmu da kuma juyayinmu yă janye zafin fushinsa don kada mu hallaka.”
[10] Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba.