Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:31

[1] Maganar Ubangiji wadda ta zo wurin Yowel ɗan Fetuwel.

[2] Ku ji wannan, ku dattawa, ku kasa kunne, dukan waɗanda suke zaune a ƙasar. Ko wani abu makamancin haka ya taɓa faruwa a kwanakinku ko a kwanakin kakanninku?

[3] Ku faɗa wa ’ya’yanku, bari kuma ’ya’yanku su faɗa wa ’ya’yansu, ’ya’yansu kuma su faɗa wa tsara ta gaba.

[4] Abin da ɗango ya bari fāri masu girma sun cinye; abin da fāri masu girma suka bari, burduduwa ta cinye; abin da burduduwa ta bari sauran kwari sun cinye.

[5] Ku farka, ku bugaggu, ku yi kuka! Ku yi kuka da ƙarfi, ku dukan mashayan ruwan inabi; ku yi kuka mai ƙarfi saboda sabon ruwan inabi, gama an riga an ƙwace ta daga leɓunanku.

[6] Wata al’umma ta mamaye ƙasata, tana da ƙarfi ba ta kuma ƙidayuwa; tana da haƙoran zaki, da zagar zakanya.

[7] Ta mayar da kuringar inabina kango ta kuma lalatar da itatuwan ɓaurena. Ta ɓamɓare bayansu duka ta kuma jefar da su ta bar rassansu fari fat.

[8] Ku yi makoki kamar budurwa a cikin tsummoki tana baƙin ciki domin mijinta na ƙuruciyarta.

[9] Hadayun hatsi da hadayun sha an yanke su daga gidan Ubangiji. Firistoci suna makoki, su waɗanda suke yi wa Ubangiji hidima.

[10] Filaye sun zama marasa amfani, ƙasa ta bushe; an lalatar da hatsi, sabon ruwan inabin ya bushe, mai kuma ba amfani.

[11] Ku fid da zuciya, ku manoma, ku yi ihu, ku masu noma inabi; ku yi baƙin ciki saboda alkama da sha’ir, saboda an lalata girbin filaye.

[12] Kuringar inabin ta bushe itacen ɓaure kuma ya yi yaushi, ’ya’yan rumman, itacen dabino da itacen gawasa, dukan itatuwan filaye, sun bushe. Tabbatacce farin cikin ’yan adam ya bushe.

[13] Ku sa tsummoki, ya firistoci, ku yi makoki; ku yi ihu, ku da kuke yin hidima a gaban bagade. Zo, ku kwana saye da tsummoki, ku waɗanda kuke yi wa Allahna hidima, gama an yanke hadayun hatsi da hadayun sha daga gidan Allahnku.

[14] Ku yi shelar azumi mai tsarki; ku kira tsarkakan taro. Ku kira dattawa da kuma dukan mazaunan ƙasar zuwa gidan Ubangiji Allahnku, ku kuma yi kuka ga Ubangiji.

[15] Kaito saboda wannan rana! Gama ranar Ubangiji ta kusa, za tă zo kamar hallaka daga wurin Maɗaukaki.

[16] Ba a yanke abinci a idanunmu, farin ciki da kuma murna daga gidan Allahnmu ba?

[17] Iri suna ta yanƙwanewa a busasshiyar ƙasa Ɗakunan ajiya sun lalace, an rurrushe rumbunan hatsin, gama hatsi ya ƙare.

[18] Ji yadda dabbobi suke nishi! Garkunan shanu sun ruɗe saboda ba su da ciyawa, har garkunan tumaki ma suna shan wahala.

[19] A gare ka, ya Ubangiji, nake kira, gama wuta ta cinye wurin kiwo harshen wuta kuma ya ƙone dukan itatuwan jeji.

[20] Har ma namun jeji suna haki gare ka; rafuffuka sun bushe wuta kuma ta cinye wurin kiwo a jeji.

Yowel — Chapters