Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 7:40

[1] Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu.

[2] Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana). Ga jerin mazan mutanen Isra’ila.

[3] Zuriyar Farosh mutum 2,172

[4] ta Shefatiya 372

[5] ta Ara 775

[6] ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812

[7] ta Elam 1,254

[8] ta Zattu 945

[9] ta Zakkai 760

[10] ta Bani 642

[11] ta Bebai 623

[12] ta Azgad 1,222

[13] ta Adonikam 666

[14] ta Bigwai 2,056

[15] ta Adin 454

[16] ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98

[17] ta Bezai 323

[18] ta Yora 112

[19] ta Hashum 223

[20] ta Gibbar 95.

[21] Mutanen Betlehem 123

[22] na Netofa 56

[23] na Anatot 128

[24] na Azmawet 42

[25] na Kiriyat Yeyarim, da Kefira Beyerot 743

[26] na Rama da Geba 621

[27] na Mikmash 122

[28] na Betel da Ai 223

[29] na Nebo 52

[30] na Magbish 156

[31] na ɗayan Elam ɗin 1,254

[32] na Harim 320

[33] na Lod, da Hadid da Ono 725

[34] na Yeriko 345

[35] na Sena’a 3,630.

[36] Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973

[37] ta Immer 1,052

[38] ta Fashhur 1,247

[39] ta Harim 1,017.

[40] Lawiyawa. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74.

[41] Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 128.

[42] Masu tsaron haikali. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139.

[43] Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot,

[44] Keros, Siyaha, Fadon,

[45] Lebana, Hagaba, Akkub,

[46] Hagab, Shamlai, Hanan,

[47] Giddel, Gahar, Reyahiya,

[48] Rezin, Nekoda, Gazzam,

[49] Uzza, Faseya, Besai,

[50] Asna, Meyunawa, Nefussiyawa,

[51] Bakbuk, Hakufa, Harhur,

[52] Bazlut, Mehida, Harsha,

[53] Barkos, Sisera, Tema,

[54] Neziya da Hatifa.

[55] Zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda,

[56] Ya’ala, Darkon, Giddel,

[57] Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Ami.

[58] Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392.

[59] Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba.

[60] ’Yan zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652.

[61] Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna).

[62] Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne.

[63] Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.

[64] Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,

[65] ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200.

[66] Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245,

[67] raƙuma 435, da jakuna 6,720.

[68] Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake.

[69] Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100.

[70] Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.

Ezra — Chapters