Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:21

[1] A daren nan, sarki bai iya barci ba, saboda haka ya ba da umarni a kawo, a kuma karanta masa littafin tarihi na shekara-shekara, da rubutaccen labarin mulkinsa.

[2] Aka tarar, a rubuce a ciki, cewa Mordekai ya tone ƙulle-ƙullen Bigtana da Teresh, biyu daga hafsoshin sarki, waɗanda suke tsaron mashigin ƙofa, waɗanda suka ƙulla su kashe Sarki Zerzes.

[3] Sarki ya ce, “Wace girma da daraja ce aka ba wa Mordekai saboda wannan?” Masu hidimarsa suka ce, “Ba a yi masa wani abu ba.”

[4] Sarki ya ce, “Wa yake a haraba?” Daidai lokacin kuwa Haman ya shigo harabar waje na fada don yă yi magana da sarki a kan a rataye Mordekai a wurin rataye mai laifin da ya shirya.

[5] Masu yi wa sarki hidima, suka amsa, “Haman yana tsaye a haraba.” Sarki ya umarta, “A kawo shi ciki.”

[6] Sa’an nan Haman ya shigo, sai sarki ya ce masa, “Me ya kamata a yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama?” Haman dai ya yi tunani a ransa ya ce, “Wane ne sarki zai girmama in ba ni ba?”

[7] Sai ya amsa wa sarki cewa, “Saboda mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama,

[8] bari a kawo rigar sarautar da sarki ya taɓa sawa, da kuma dokin da sarki ya taɓa hawa, wanda aka sa kambin sarauta a kai.

[9] Sa’an nan, bari a ba da rigar da kuma dokin wa ɗaya daga cikin manyan sarakuna mafi kirki na sarki. Bari shi kuma yă sa wannan riga wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama, a kuma bi da shi a bisan doki ko’ina a titunan birni, ana shela a gabansa ana cewa, ‘Wannan shi ne abin da ake yin wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!’ ”

[10] Sarki ya umarci Haman ya ce, “Tafi yanzu ka karɓi rigar da dokin, ka kuma yi yadda ka shawarta wa Mordekai, mutumin Yahudan nan, wanda yake zama a bakin ƙofar sarki. Kada ka kāsa yin kome daga cikin abin da ka faɗa.”

[11] Saboda haka, Haman ya karɓo rigar da dokin. Ya sa wa Mordekai rigar, ya kuma bi da shi a kan doki ko’ina a titunan birnin, yana shela a gabansa yana cewa, “Wannan shi ne abin da ake yi wa mutumin da sarki yake jin daɗi yă girmama!”

[12] Daga baya, Mordekai ya dawo zuwa ƙofar sarki. Amma Haman ya ruga gida, kansa a rufe, saboda baƙin ciki.

[13] Ya je ya faɗa wa matarsa Zeresh, da dukan abokansa, me ya same shi. Masu ba shi shawara, da matarsa Zeresh, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara fāɗuwa a gabansa, daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, tabbatacce za ka fāɗi a gabansa!”

[14] Suna cikin magana da shi ke nan, sai ga bābānnin sarki, suka iso suka kuma hanzarta da Haman zuwa liyafar da Esta ta shirya.

Esta — Chapters