[1] Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya,
[2] ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu, har ya ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.
[3] Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba.
[4] Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana, ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya.
[5] Ku dai tabbata, ba wani mai fasikanci, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah.
[6] Kada wani yă ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya.
[7] Saboda haka kada ku haɗa kai da su.
[8] Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske
[9] (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya)
[10] ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.
[11] Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su.
[12] Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.
[13] Duk abin da aka kawo a gaban haske ana iya ganinsa, kuma duk abin da aka haskaka yakan zama haske.
[14] Shi ya sa aka ce, “Ka farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu, Kiristi kuwa zai haskaka ka.”
[15] Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai kamar masu hikima.
[16] Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin nan mugaye ne.
[17] Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.
[18] Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu.
[19] Ku yi zance da juna cikin zabura, da waƙoƙi, da kuma waƙoƙin ruhaniya. Ku rera, ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji.
[20] Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi, kuna gode wa Allah Uba a kome.
[21] Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke nuna wa Kiristi.
[22] Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, kamar ga Ubangiji ne kuke yi.
[23] Gama miji shi ne kan mace, yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa.
[24] To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.
[25] Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta.
[26] Ya mai da ikkilisiya ta zama mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa.
[27] Kiristi ya yi haka don yă miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma mai tsarki, marar aibi, marar tabo, da kuma marar lahani.
[28] Don haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar yadda suke ƙaunar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa, yana ƙaunar kansa ne.
[29] Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yă ciyar da shi, yă kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya,
[30] gama mu gaɓoɓin jikinsa ne.
[31] “Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.”
[32] Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya.
[33] Duk da haka, dole kowannenku yă ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar tă yi biyayya ga mijinta.