Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:38

[1] Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona, da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne, ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya, waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!

[2] Ku je Kalne ku dube ta; ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba, sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya. Sun fi masarautunku biyu ne? Ƙasarsu ta fi taku girma?

[3] Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar rana kuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa.

[4] Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwa kuna mimmiƙe a kan kujerunku. Kuna cin naman ƙibabbun raguna da na ƙosassun ’yan maruƙa.

[5] Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yi kuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.

[6] Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabi kuna kuma shafa mai mafi kyau, amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.

[7] Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta; bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.

[8] Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta, “Ina ƙyamar girman kan Yaƙub, ba na kuma son kagarunsa; zan ba da birnin da duk abin da yake cikinta.”

[9] Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu.

[10] In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”

[11] Gama Ubangiji ya ba da umarni, zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucu ƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.

[12] Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu? Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma? Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafi amfanin adalci kuma ya zama ɗaci,

[13] ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar da yaƙi kuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim ba?”

[14] Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce, “Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila, wadda za tă matsa muku tun daga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba.”

Amos — Chapters