[1] Manzanni da ’yan’uwa ko’ina a Yahudiya suka ji cewa Al’ummai ma sun karɓi maganar Allah.
[2] Saboda haka sa’ad da Bitrus ya haura zuwa Urushalima, masu bin da suke da kaciya suka zarge shi
[3] suka ce, “Ka je gidan mutanen da suke marasa kaciya ka kuwa ci tare da su.”
[4] Bitrus ya fara yin musu bayani dalla-dalla yadda ya faru cewa,
[5] “Ina a birnin Yoffa ina addu’a, sai ga wahayi ya zo mini. Na ga ana sauko da wani abu kamar babban mayafi daga sama ta kusurwansa huɗu, ya kuma sauko inda nake.
[6] Na duba cikinsa na ga dabbobi masu ƙafa huɗu na duniya, da namun jeji, da masu ja da ciki, da kuma tsuntsayen sararin sama.
[7] Sa’an nan na ji wata murya tana ce mini, ‘Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.’
[8] “Na amsa na ce, ‘Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.’
[9] “Sai muryar daga sama ta yi magana sau na biyu, ta ce, ‘Kada ka ce da abin da Allah ya tsarkake marar tsarki.’
[10] Wannan ya faru har sau uku, sa’an nan duk aka sāke ɗauke shi zuwa sama.
[11] “Nan take sai ga mutum uku da aka aika wurina daga Kaisariya a tsaye a ƙofar gidan da nake.
[12] Ruhu ya ce mini kada in yi wata-wata game da tafiya tare da su. Waɗannan ’yan’uwa guda shida su ma suka rako ni, muka kuwa shiga gidan mutumin.
[13] Ya kuma gaya mana yadda wani mala’ika ya bayyana a gidansa ya ce masa, ‘Ka aika zuwa Yoffa a kira Siman wanda ake ce da shi Bitrus.
[14] Zai kawo maka saƙo wanda ta wurinsa kai da dukan iyalinka za ku sami ceto.’
[15] “Na fara magana ke nan, sai Ruhu Mai Tsarki ya sauko musu yadda ya sauko mana a farko.
[16] Sa’an nan na tuna da abin da Ubangiji ya ce, ‘Yohanna ya yi baftisma da ruwa, amma za a yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’
[17] To, in Allah ya ba su kyauta yadda ya ba mu, mu da muka gaskata da Ubangiji Yesu Kiristi, wane ni da zan yi hamayya da Allah?”
[18] Sa’ad da suka ji haka, ba su ƙara yin faɗa ba, suka kuma ɗaukaka Allah, suna cewa, “To, fa, har Al’ummai ma Allah ya sa suka tuba zuwa rai.”
[19] To, waɗanda suka warwatsu saboda tsananin da ya tashi a kan batun Istifanus suka tafi har Funisiya, Saifurus da kuma Antiyok, suna ba da saƙon ga Yahudawa kaɗai.
[20] Amma waɗansunsu kuwa, mutane daga Saifurus da Sairin, suka je Antiyok suka fara yi wa Hellenawa magana su ma, suna ba da labari mai daɗi game da Ubangiji Yesu.
[21] Hannun Ubangiji kuwa yana tare da su, mutane da yawan gaske kuwa suka gaskata suka juya ga Ubangiji.
[22] Labari wannan abu ya kai kunnuwan ikkilisiya a Urushalima, sai suka aiki Barnabas zuwa Antiyok.
[23] Da ya iso ya kuma ga tabbacin alherin Allah, sai ya yi farin ciki ya kuma ƙarfafa su duka su tsaya da gaskiya cikin Ubangiji da dukan zukatansu.
[24] Mutum ne nagari, cike da Ruhu Mai Tsarki da bangaskiya, mutane masu yawan gaske kuwa suka juya ga Ubangiji.
[25] Sa’an nan Barnabas ya tafi Tarshish don yă nemi Shawulu,
[26] sa’ad da ya same shi kuwa, sai ya kawo shi Antiyok. Ta haka shekara guda cur Barnabas da Shawulu suka yi suna taruwa da ikkilisiya, suka kuma koya wa mutane masu yawan gaske. A Antiyok ne aka fara kiran almajirai da suna Kirista.
[27] A wannan lokaci waɗansu annabawa sun zo Antiyok daga Urushalima.
[28] Ɗaya daga cikinsu mai suna Agabus, ya miƙe tsaye ya yi annabci ta wurin Ruhu cewa za a yi yunwa mai tsanani wadda za tă bazu a dukan duniyar Romawa (Wannan ya faru a zamanin mulkin Kalaudiyus.)
[29] Kowanne a cikin almajiran, gwargwadon azancinsa, ya yanke shawara ya ba da gudummawa ga ’yan’uwan da suke zama a Yahudiya.
[30] Haka kuwa suka yi, suka aika da kyautarsa wa dattawan ikkilisiyar ta hannu Barnabas da Shawulu.