[1] A gaban Allah da kuma Kiristi Yesu, wanda zai yi wa masu rai da matattu shari’a, saboda kuma bayyanuwarsa da mulkinsa, ina ba ka umarni.
[2] Ka yi wa’azin Maganar Allah, ka zama a shirye a kullum, ko da zarafi, ko babu zarafi, ka yi gyara, ka kwaɓe, ka kuma ƙarfafa, da matuƙar haƙuri da koyarwa cikin natsuwa.
[3] Gama lokaci yana zuwa da mutane ba za su jure da sahihiyar koyarwa ba. A maimako, don cimma burinsu, za su taro wa kansu malamai masu yawa, domin su faɗi abin da kunnuwansu masu ƙaiƙayi suke so su ji.
[4] Za su juye kunnuwansu daga gaskiya zuwa ga jin tatsuniyoyi.
[5] Amma kai, ka natsu cikin kowane hali, ka jure shan wahala, ka yi aikin mai bishara, ka cika dukan ayyukan hidimarka.
[6] Gama an riga an tsiyaye ni kamar hadaya ta sha, kuma lokacin tashina ya yi.
[7] Na yi fama mai kyau, na gama tseren, na riƙe bangaskiya.
[8] Yanzu kuwa an ajiye mini rawanin adalci, wanda Ubangiji, Alƙali mai adalci zai ba ni a ranan nan ba kuwa ni kaɗai ba, amma ga duk waɗanda suka yi marmarin bayyanuwarsa.
[9] Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka zo wurina da sauri,
[10] gama Demas, saboda ƙaunar wannan duniya, ya yashe ni ya tafi Tessalonika. Kirssens ya tafi Galatiya, Titus kuwa ya tafi Dalmatiya.
[11] Luka ne kaɗai yake tare da ni. Ka nemi Markus ku zo tare, domin yana da amfani a gare ni cikin hidimata.
[12] Na aiki Tikikus zuwa Afisa.
[13] Sa’ad da za ka dawo, ka zo mini da alkyabbar da na bari a wurin Karbus a Toruwas, da kuma naɗaɗɗun littattafaina, tun ba ma fatun nan masu rubutu ba.
[14] Alekzanda maƙerin ƙarafan nan ya yi mini mugunta ƙwarai. Ubangiji zai sāka masa saboda abin da ya yi.
[15] Kai ma sai ka lura da shi, domin ya yi gāba sosai da saƙonmu.
[16] A lokacin da na kāre kaina da farko, ba wanda ya goyi bayana, sai ma kowa ya yashe ni. Ina fata ba za a lasafta wannan laifi a kansu ba.
[17] Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki.
[18] Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.
[19] Ka gai da Firiskila da Akwila da iyalin Onesiforus.
[20] Erastus ya dakata a Korint, na kuma bar Turofimus cikin rashin lafiya a Miletus.
[21] Ka yi iyakacin ƙoƙarinka ka iso nan kafin damina. Yubulus yana gaishe ka, haka ma Fuden, Lainus, Kalaudiya da kuma dukan ’yan’uwa.
[22] Ubangiji yă zama tare da ruhunka. Alheri yă zama tare da ku.