Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 6:51

[1] Dawuda ya rera wannan waƙa ga Ubangiji, sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa, da kuma daga hannun Shawulu.

[2] Ya ce, “Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona;

[3] Allahna shi ne dutsena. A gare shi nake samun kāriya shi ne garkuwata da kuma ƙahon cetona. Shi ne mafakata, maɓuyata, da mai cetona. Daga mutane masu fitina, ka cece ni.

[4] “Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa tsira daga abokan gābana.

[5] Raƙumar ruwan mutuwa sun kewaye ni; raƙumar ruwan hallaka suna cin ƙarfina.

[6] Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni; tarkuna kuma suka auka mini.

[7] “A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; na yi kira ga Allahna. Daga cikin haikalinsa ya saurare muryata; kukata ta zo kunnensa.

[8] Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, harsashan sararin sama sun jijjigu; suka yi makyarkyata saboda yana fushi.

[9] Hayaƙi ya taso daga kafaffen hancinsa; harshen wuta mai cinyewa daga bakinsa, garwashi mai ƙuna daga bakinsa.

[10] Ya buɗe sararin sama, ya sauko ƙasa, girgije mai duhu suna ƙarƙashin ƙafafunsa.

[11] Ya hau kerubobi, ya tashi sama; ya yi firiya a fikafikan iska.

[12] Ya mai da duhu abin rufuwarsa gizagizai masu kauri cike da ruwa suka kewaye shi.

[13] Daga cikin hasken gabansa garwashi wuta mai ci ya yi walƙiya.

[14] Ubangiji ya yi tsawa daga sararin sama; aka ji muryar Mafi Ɗaukaka.

[15] Ya harbe kibiyoyi, ya wartsar da abokan gāba, da walƙiya kuma ya sa suka gudu.

[16] Aka bayyana kwarin teku, tushen duniya suka tonu. A tsawatawar Ubangiji, da numfashinsa mai ƙarfi daga hancinsa.

[17] “Daga sama ya miƙo hannu ya ɗauke ni, ya tsamo ni daga zurfafa ruwaye.

[18] Ya kuɓutar da ni daga hannun abokin gāba mai iko, daga maƙiyina da suka fi ƙarfina.

[19] Suka auka mini cikin ranar masifata, amma Ubangiji ya kiyaye ni.

[20] Ya fito da ni, ya kai ni wuri mafi fāɗi; ya kuɓutar da ni gama yana jin daɗina.

[21] “Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya sāka mini.

[22] Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi wani mugun abu da zai juyar da ni daga Allahna ba.

[23] Dukan dokokinsa suna a gabana; ban ƙi ko ɗaya daga umarnansa ba.

[24] Ba ni da laifi a gabansa na kiyaye kaina daga yin zunubi.

[25] Ubangiji ya sāka mini bisa ga adalcina bisa ga tsarkina a gabansa.

[26] “Ga masu aminci, kakan nuna kanka mai aminci, ga marasa laifi, kakan nuna kanka marar laifi,

[27] ga masu tsarki, kakan nuna musu tsarki. Amma ga masu karkataccen hali, kakan nuna kanka mai wayo.

[28] Kakan ceci mai tawali’u, amma idanunka suna a kan masu girman kai don ka ƙasƙantar da su.

[29] Ya Ubangiji kai ne fitilata; Ubangiji ya mai da duhuna haske.

[30] Da taimakonka zan iya auka wa rundunar sojoji; tare da Allahna zan iya hawan katanga.

[31] “Ga Allah dai, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji babu kuskure. Shi garkuwa ce ga waɗanda suka nemi mafaka a gare shi.

[32] Gama wane ne Allah, in ba Ubangiji ba? Wane ne dutse kuma in ba Allahnmu ba?

[33] Allah ne ya ba ni ƙarfi, ya kuma mai da hanyata cikakkiya.

[34] Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsayawa a kan duwatsu.

[35] Ya hori hannuwana don yaƙi, hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.

[36] Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.

[37] Ka fadada hanya a ƙarƙashina domin kada idon ƙafana yă juya.

[38] “Na fafari abokan gābana, na murƙushe su; ban kuwa juya ba sai da na hallaka su.

[39] Na hallaka su ƙaƙaf, ba kuwa za su ƙara tashi ba, sun fāɗi a ƙarƙashin sawuna.

[40] Ka ba ni ƙarfi don yaƙi; ka sa maƙiyina suka rusuna a ƙafafuna.

[41] Ka sa abokan gābana suka juya a guje, na kuwa hallaka maƙiyina.

[42] Suka nemi taimako, amma babu wanda zai cece su, suka yi kira ga Ubangiji, amma ba a amsa musu ba.

[43] Na murƙushe su, suka yi laushi kamar ƙura; na daka na kuma tattake su kamar caɓi a kan tituna.

[44] “Ka kuɓutar da ni daga harin mutanena; ka kiyaye ni kamar shugaban al’ummai. Mutanen da ban sansu ba za su kasance a ƙarƙashina,

[45] baƙi kuma su na zuwa don su yi mini fadanci; da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya.

[46] Zukatansu ta karaya; suka fito da rawan jiki daga kagararsu.

[47] “Ubangiji yana a raye! Yabo ta tabbata ga Dutsena! Ɗaukaka ga Allah, Dutse, Mai Cetona!

[48] Shi ne Allahn da yake rama mini, wanda ya sa al’ummai a ƙarƙashina,

[49] wanda ya kuɓutar da ni daga maƙiyina. Ka ɗaukaka ni bisa maƙiyina; ka kiyaye ni daga hannun mugayen mutane.

[50] Saboda haka, zan yabe ka, ya Ubangiji cikin dukan al’ummai; Zan rera waƙoƙin yabo ga sunanka.

[51] “Ya ba wa sarkinsa kyakkyawan nasara; ya nuna madawwamiyar ƙauna ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.”

2 Sama’ila — Chapters