Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 4:17

[1] Amma a dā akwai annabawan ƙarya a cikin mutane, kamar yadda za a sami malaman ƙarya a cikinku. A ɓoye za su shigar da karkataccen koyarwa mai hallaka, har ma su yi mūsun Ubangiji mai iko duka wanda ya saye su suna kawo wa kansu hallaka farat ɗaya.

[2] Da yawa za su bi hanyoyinsu na rashin kunya su kuma sa a rena hanyar gaskiya.

[3] Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.

[4] Gama in har Allah bai ƙyale mala’iku sa’ad da suka yi zunubi ba, amma ya tura su cikin lahira, domin a tsare su don hukunci;

[5] in har bai ƙyale duniya ta dā ba sa’ad da ya kawo ambaliya a kan mutanenta marasa tsoron Allah, amma ya kiyaye Nuhu, mai wa’azin adalci, da kuma waɗansu bakwai;

[6] in har ya hukunta biranen Sodom da Gomorra ta wurin ƙone su suka zama toka, ya kuma maishe su misali na abin da zai faru da marasa tsoron Allah;

[7] in kuwa har ya ceci Lot, mai adalci, wanda ya damu ainun da ƙazamar rayuwar mutane marasa bin doka;

[8] (adon kuwa abin da adalin nan ya yi, ya kuma gani, sa’ad da yake a cikinsu, sai kowace rana yakan ji ciwon aikinsu na kangara a zuciyarsa mai adalci)

[9] in haka ne, to, Ubangiji ya san yadda zai ceci mutane masu tsoron Allah daga gwaje-gwaje, yă kuma tsare marasa adalci don ranar hukunci, har yă zuwa ranar shari’a.

[10] Wannan gaskiya ce musamman ga waɗanda suke bin sha’awace-sha’awacen lalaci na mutuntaka, suna kuma rena masu mulki. Da ƙarfin hali da kuma girman kai, waɗannan mutane ba sa tsoro kawo zargin ɓata sunan talikan sama;

[11] duk da haka ko mala’iku ma da suka fi su ƙarfi suka kuma fi su iko, ba sa kawo irin wannan zargi na ɓata suna game da waɗannan talikai a gaban Ubangiji.

[12] Amma waɗannan mutane suna yin saɓo a kan abubuwan da ba su fahimta ba. Suna kama da dabbobi marasa hankali, halittun da suke bin abin da jikinsu ya faɗa musu kawai, waɗanda aka haifa don a kama a hallaka, kuma kamar dabbobi su ma za su hallaka.

[13] Za a yi musu sakamako da muguntar da suka yi. A ra’ayinsu jin daɗi shi ne a yi annashuwa da rana tsaka. Su ƙazamai ne marasa kunya, suna cike da jin daɗin sha’awace-sha’awacensu yayinda suke cin biki tare da ku.

[14] Idanunsu sun cike da zina, ba sa ƙoshi da yin zunubi; suna jarrabtar waɗanda ba tsayayyu ba; gwanaye ne a kan kwaɗayi, la’anannun iri!

[15] Sun bar miƙaƙƙiyar hanya suka bauɗe suna bin hanyar Bala’am ɗan Beyor, wanda ya yi ƙaunar hakkin mugunta.

[16] Amma an tsawata masa saboda laifinsa ta wurin jaki, dabbar da ba ta magana, wadda ta yi magana da muryar mutum ta kuma kwaɓi haukan annabin.

[17] Waɗannan mutane maɓulɓulai ne babu ruwa da kuma hazon da guguwar iska take kora. An shirya matsanancin duhu dominsu.

[18] Gama suna surutai banza na girman kai, ta wurin son bin fasikanci na mutuntaka, sukan jan hankulan mutanen da suke kuɓucewa daga waɗancan masu zama cikin kuskure.

[19] Suna yin musu alkawarin ’yanci, yayinda su kansu bayi ne ga aikin lalata gama mutum bawa ne ga duk abin da ya mallake shi.

[20] In har sun kuɓuta daga lalacin duniya ta wurin sanin Ubangijinmu da kuma Mai Cetonmu Yesu Kiristi sai suka sāke koma a cikin lalacin, har ya rinjaye su, za su fi muni a ƙarshe fiye da farko.

[21] Zai fi musu kyau da ba su taɓa sanin hanyar adalci ba, fiye da a ce sun sani sa’an nan su juya bayansu ga umarni mai tsarkin nan da aka ba su.

[22] A kansu karin maganan nan gaskiya ce, “Kare ya koma kan amansa,” da kuma, “Alade da aka yi wa wanka, ya koma birgimarsa cikin laka.”

2 Bitrus — Chapters