Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:14

[1] Babu wata bukata in rubuta muku game da hidiman nan ga tsarkaka.

[2] Gama na san aniyarku na yin taimako, ina kuma taƙama a kan wannan ga Makidoniyawa, ina faɗin musu cewa tun bara, ku da kuke a Akayya a shirye kuke ku bayar. Ƙoƙarinku kuwa ya zuga yawancinsu ga aiki.

[3] Amma ina aika ’yan’uwan nan don kada taƙamar da muke yi da ku, a kan wannan al’amari ta zama a banza, sai dai domin yă zama kuna nan a shirye, kamar yadda na faɗa za ku kasance.

[4] Gama in waɗansu mutanen Makidoniya sun zo tare da ni, suka tarar ba a shirye kuke ba, kunya ta ishe mu, balle fa ku, saboda amincewa da muke yi da ku.

[5] Saboda haka, na ga ya dace in roƙi ’yan’uwan nan su ziyarce ku kafin lokacin, su kuma gama shirye-shirye saboda bayarwa ta yardar ran da kuka yi alkawari. Ta haka bayarwar za tă zama a shirye, ta yardar rai ba ta dole ba.

[6] Ku tuna fa, duk wanda ya yi shuki kaɗan zai girbe kaɗan, kuma duk wanda ya yi shuki da yawa, zai girbe a yalwace.

[7] Ya kamata kowa yă bayar bisa ga abin da ya yi shawara a zuciyarsa, ba tare da jin nauyi ko don dole ba, gama Allah yana son mai bayarwa da daɗin rai.

[8] Allah kuwa yana da iko yă ba ku fiye da bukatarku, domin kullum ku wadata da kome ta kowace hanya, kuna ta bayarwa hannu sake, kowane irin kyakkyawan aiki.

[9] Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, ayyukansa na alheri madawwama ne.”

[10] To, shi da yake ba mai shuka iri, yake kuma ba da abinci a ci, shi ne zai ba ku irin shukawa, yă riɓanya shi, yă kuma albarkaci ayyukanku na alheri da yawa.

[11] Za a wadatar da ku ta kowace hanya, domin ku riƙa bayarwa hannu sake a kowane lokaci. Ta wurinmu kuma bayarwarku hannu sake za tă zama sanadin godiya ga Allah.

[12] Wannan hidimar da kuke yi, ba bukatun mutanen Allah kaɗai take biya ba, amma tana cike da hanyoyin nuna godiya masu yawa ga Allah.

[13] Aikin nan naku na alheri tabbatar bangaskiyarku ne, za a kuwa ɗaukaka Allah saboda kun bayyana yarda, cewa kun yi na’am da bisharar Kiristi, saboda kuma gudummawa da kuka yi musu da saura duka, hannu sake.

[14] A cikin addu’arsu dominku kuwa, zukatansu za su koma gare ku, saboda mafificin alherin da Allah ya ba ku.

[15] Godiya ga Allah, saboda kyautarsa da ta wuce misali!

2 Korintiyawa — Chapters