Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:30

[1] Sa’ad da Rehobowam ya iso Urushalima, ya tattara mayaƙa dubu ɗari takwas daga gidan Yahuda da Benyamin, don su yi yaƙi da Isra’ila su sāke mai da mulki wa Rehobowam.

[2] Amma wannan maganar Ubangiji ta zo ga Shemahiya mutumin Allah.

[3] “Faɗa wa Rehobowam ɗan Solomon sarkin Yahuda da kuma dukan Isra’ilawan da suke a Yahuda da Benyamin,

[4] ‘Ga abin da Ubangiji ya ce kada ku haura don ku yi yaƙi da ’yan’uwanku. Ku tafi gida kowannenku, gama wannan yi na ne.’ ” Saboda haka suka yi biyayya ga maganar Ubangiji suka kuma koma daga takawa don yaƙi da Yerobowam.

[5] Rehobowam ya zauna a Urushalima ya kuma gina garuruwa don kāriya a cikin Yahuda.

[6] Betlehem, Etam, Tekowa,

[7] Bet-Zur, Soko, Adullam,

[8] Gat, Maresha, Zif,

[9] Adorayim, Lakish, Azeka,

[10] Zora, Aiyalon da Hebron. Waɗannan su ne garuruwan katanga a cikin Yahuda da Benyamin.

[11] Ya ƙarfafa kāriyarsu ya kuma sa shugabannin mayaƙa a cikinsu, tare da tanadin abinci, man zaitun da kuma ruwan inabi.

[12] Ya sa garkuwoyi da māsu a cikin dukan biranen, ya kuma sa suka zama da ƙarfi. Saboda haka Yahuda da Benyamin suka zama nasa.

[13] Firistoci da Lawiyawa daga dukan yankuna ko’ina a Isra’ila suka haɗa kai da shi.

[14] Lawiyawa suka ma bar makiyayansu da mallakarsu, suka zo Yahuda da Urushalima domin Yerobowam da ’ya’yansa maza sun ƙi su a matsayin firistocin Ubangiji.

[15] Yerobowam ya naɗa firistocinsa domin masujadan kan tudu da kuma domin gumakan nan na akuya da maraƙin da ya yi.

[16] Waɗanda suke daga kowane kabilar Isra’ila waɗanda suka sa zuciya a kan neman Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka bi Lawiyawa zuwa Urushalima don su miƙa hadayu ga Ubangiji Allah na kakanninsu.

[17] Suka ƙarfafa mulkin Yahuda suka kuma goyi bayan Rehobowam ɗan Solomon shekaru uku, suna tafiya a hanyoyin Dawuda da Solomon a wannan lokaci.

[18] Rehobowam ya auri Mahalat, ’yar Yerimot ɗan Dawuda wadda Abihayil ’yar Eliyab ɗan Yesse ta haifa.

[19] Ta haifa masa ’ya’ya maza. Yewush, Shemariya da Zaham.

[20] Sa’an nan ya auri Ma’aka ’yar Absalom, wadda ta haifa masa Abiya, Attai, Ziza da kuma Shelomit.

[21] Rehobowam ya ƙaunaci Ma’aka ’yar Absalom fiye da sauran matansa da ƙwarƙwaransa. Duka-duka dai ya auri mata goma sha takwas da ƙwarƙwarai sittin, yana da ’ya’ya maza ashirin da takwas da ’ya’ya mata sittin.

[22] Rehobowam ya naɗa Abiya ɗan Ma’aka yă zama babba yerima a cikin ’yan’uwansa, don dai yă naɗa shi sarki.

[23] Ya yi hikima, ya watsar da waɗansu ’ya’yansa a dukan yankunan Yahuda da Benyamin, da kuma a dukan birane masu katanga. Ya ba su tanadi mai yawa ya kuma aurar musu mata masu yawa.

2 Tarihi — Chapters