[1] To, ’yan’uwa, game da lokuta da ranaku, ba ma bukata mu rubuta muku,
[2] gama kun sani sarai cewa ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo da dare.
[3] Yayinda mutane suke cewa, “Akwai salama da zaman lafiya,” hallaka za tă auko musu farat ɗaya, kamar yadda naƙuda take kama mace mai ciki, ba za su kuwa tsira ba.
[4] Amma ku, ’yan’uwa, ba kwa cikin duhu da wannan rana za tă zo muku ba zato kamar ɓarawo.
[5] Dukanku ’ya’yan haske ne da kuma ’ya’yan rana. Mu ba mutanen dare ko na duhu ba ne.
[6] Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai.
[7] Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa.
[8] Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano.
[9] Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
[10] Ya mutu saboda mu domin, ko muna a faɗake ko muna barci, mu kasance tare da shi.
[11] Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.
[12] To, muna roƙonku, ’yan’uwa, ku girmama waɗanda suke aiki sosai a cikinku, waɗanda suke bisanku cikin Ubangiji da kuma waɗanda suke yin muku gargaɗi.
[13] Ku riƙe su da mutunci sosai cikin ƙauna saboda aikinsu. Ku yi zaman lafiya da juna.
[14] Muna kuma gargaɗe ku, ’yan’uwa, ku gargaɗe waɗanda suke zaman banza, ku ƙarfafa masu raunanar zuciya, ku taimaki marasa ƙarfi, ku yi haƙuri da kowa.
[15] Ku tabbata cewa kada kowa yă rama mugunta da mugunta, sai dai kullum ku yi ƙoƙarin yin wa juna alheri da kuma dukan mutane.
[16] Ku riƙa farin ciki kullum;
[17] ku ci gaba da yin addu’a;
[18] ku yi godiya cikin kowane hali, gama wannan shi ne nufin Allah dominku cikin Kiristi Yesu.
[19] Kada ku danne aikin Ruhu.
[20] Kada ku rena annabci,
[21] amma ku gwada kome, ku riƙe abin da yake mai kyau,
[22] ku ƙi kowace mugunta.
[23] Bari Allah da kansa, Allah na salama, yă tsarkake ku sarai. Bari dukan ruhunku, ranku, da kuma jikinku su zama marar aibi a dawowar Ubangijinmu Yesu Kiristi.
[24] Wannan wanda ya kira ku mai aminci ne zai kuwa aikata.
[25] ’Yan’uwa, ku yi mana addu’a.
[26] Ku gaggai da dukan ’yan’uwa da sumba mai tsarki.
[27] Na gama ku da Ubangiji ku sa a karanta wannan wasiƙa ga dukan ’yan’uwa.
[28] Alherin Ubangijinmu Yesu Kiristi yă kasance tare da ku.