[1] Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.
[2] Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba.
[3] Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.
[4] Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama.
[5] Suka ce masa, “Ka tsufa, ’ya’yanka kuma ba sa bin hanyarka, saboda haka sai ka naɗa sarkin da zai bi da mu kamar yadda sauran ƙasashe suke da su.”
[6] Amma Sama’ila bai ji daɗi sa’ad da suka ce, “Ka ba mu sarki da zai bi da mu.” Sai ya yi addu’a ga Ubangiji.
[7] Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka saurari dukan maganganun da mutanen suke gaya maka. Ai, ba kai ba ne suka ƙi, ni ne suka ƙi in zama sarkinsu.
[8] Haka suka yi daga tun daga ranar da na fitar da su daga Masar har zuwa yau, suka ƙi ni, suka bauta wa waɗansu alloli, haka ma suke yi maka.
[9] Yanzu ka saurare su amma ka yi musu kashedi sosai, ka sa su san abin da sarkin da zai bi da su zai yi.”
[10] Sama’ila kuwa ya ce wa mutanen da suke roƙo yă naɗa musu sarki dukan abin da Ubangiji ya faɗa.
[11] Ya ce musu, “Ga abin da sarkin da zai yi mulkinku zai yi. Zai kwashe ’ya’yanku yă sa su yi aiki da kekunan yaƙi da dawakansa, waɗansu za su riƙa gudu a gaban keken yaƙinsa.
[12] Zai sa waɗansu su zama shugabannin mutum dubu-dubu da kuma na hamsin-hamsin. Waɗansu za su yi masa noma da girbi. Waɗansu za su ƙera masa makaman yaƙi da kayayyaki don keken yaƙinsa.
[13] Zai sa ’ya’yanku mata yin aikin turare da dafe-dafe da kuma toye-toye.
[14] Zai karɓi gonakinku mafi kyau da gonakin inabinku da gonakin zaitunku yă ba wa ma’aikatansa.
[15] Zai kuma karɓi zakan hatsinku da na inabinku yă ba shugabannin fadarsa da sauran masu hidimarsa.
[16] Zai ƙwace bayinku maza da mata, da shanunku, da jakunanku mafi kyau domin su yi masa aiki.
[17] Zai karɓi zakan dabbobinku, ku kanku za ku zama bayinsa.
[18] Sa’ad da ranar ta zo, za ku yi kuka ku nemi a fishe ku daga sarkin da kuka zaɓa, Ubangiji kuwa ba zai ji ku ba.”
[19] Amma mutanen suka ƙi jin Sama’ila, sai suka ce, “A’a, mu dai, muna son sarki yă bi da mu.”
[20] Ta haka za mu zama kamar sauran ƙasashe, mu kasance da sarkin da zai bi da mu, yă tafi tare da mu zuwa yaƙe-yaƙe.
[21] Da Sama’ila ya ji duk maganganun da mutanen suka faɗa, sai ya mayar wa Ubangiji.
[22] Ubangiji kuwa ya ce, “Ka saurare su, ka naɗa masu sarki.” Sa’an nan Sama’ila ya ce wa mutanen Isra’ila, “Kowa yă koma garinsa.”