Skip to content
Opens in a new window
Listen to this chapter • 3:16

[1] Saboda haka, da yake Kiristi ya sha wahala a jikinsa, sai ku ma ku yi wa kanku ɗamara da irin wannan hali, gama wanda ya sha wahala a jikinsa ya gama da zunubi ke nan.

[2] Ta haka, ba ya sauran rayuwarsa a kan mugayen sha’awace-sha’awacen jiki, sai dai nufin Allah.

[3] Gama kun ɓata lokaci sosai a dā kuna yin abubuwan da masu bauta gumaka suka zaɓa su yi, kuna rayuwa cikin lalata, sha’awace-sha’awace, buguwa, shashanci, shaye-shaye da kuma bautar gumaka masu banƙyama.

[4] Sun yi mamaki da ba kwa haɗa kai da su a yanzu, da ba kwa kutsa kai tare da su cikin irin rayuwar banzan nan, har suna zaginku.

[5] Amma dole su ba da lissafi gare shi wanda yake a shirye yă shari’anta masu rai da matattu.

[6] Dalilin ke nan da ya sa aka yi wa’azin bishara har ga waɗanda yanzu suke mutattu, don ko da yake an hukunta su a matsayin mutane a batun jiki, amma su rayu ga Allah a batun ruhu.

[7] Ƙarshen abubuwa duka ya yi kusa. Saboda haka ku kasance masu tunani mai kyau da masu kamunkai don ku iya yin addu’a.

[8] Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

[9] Ku riƙa karɓar juna ba da gunaguni ba.

[10] Kowa yă yi amfani da kowace baiwar da ya samu don kyautata wa waɗansu, cikin aminci yana aikata alherin Allah a hanyoyi dabam-dabam.

[11] In wani ya yi magana, ya kamata yă yi ta a matsayin wanda yake magana ainihin kalmomin Allah. In wani yana yin hidima, ya kamata yă yi ta da ƙarfin da Allah ya tanadar, domin a cikin kome a yabi Allah ta wurin Yesu Kiristi. A gare shi ɗaukaka da iko sun tabbata har abada abadin. Amin.

[12] Abokaina ƙaunatattu, kada ku yi mamakin gwaji mai tsananin da kuke sha, sai ka ce wani baƙon abu ne yake faruwa da ku.

[13] Sai dai ku yi murna cewa kuna tarayya cikin shan wahalolin Kiristi, domin ku kai ga farin ciki mai yawa sa’ad da aka bayyana ɗaukakarsa.

[14] In an zage ku saboda sunan Kiristi, ku masu albarka ne, gama Ruhun ɗaukaka da kuma na Allah yana bisanku.

[15] In kuna shan wahala, kada yă zama don ku masu kisankai ne ko ɓarayi ko masu wani irin laifi ko kuma masu shisshigi.

[16] Amma fa, in kuka sha wahala a matsayin ku Kirista ne, kada ku ji kunya, sai dai ku yabi Allah cewa kuna amsa wannan suna.

[17] Gama lokaci ya yi da za a fara yi wa iyalin Allah shari’a; in kuwa ya fara da mu, to, me zai faru da waɗanda ba sa biyayya da bisharar Allah?

[18] Kuma, “In da ƙyar masu adalci su kuɓuta, me zai faru da marasa tsoron Allah da kuma masu zunubi?”

[19] Saboda haka, waɗanda suke shan wahala bisa ga nufin Allah ya kamata su danƙa kansu ga Mahaliccinsu mai aminci, su kuma ci gaba da aikata abin da yake daidai.

1 Bitrus — Chapters