Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya maida hankali kan wasan El-Clasico da aka yi tsakanin Barcelona da Real Madrid. Shi dai wasa tsakanin waɗannan ƙungiyoyi ba wai wasa bane na gama gari, domin yanada ɗinbin tarihi ganin cewa an faro shine a shekarar 1902, kuma wancan lokacin Barcelona ce ta fara samun nasara kan Madrid da ci 3-1. Sai dai a wasan na daren jiya Lahadi Madrid ce ta samu nasara da ci 2-1.
Sakamakon wannan wasa ya bada mamaki matuƙa, domin dai an yi tunanin Barcelona za ta yi wa Madrid Kukkunge ne, kasancewar tana gida tare da goyon bayan mutane dubu 62,650 da suka taru a filin wasan Spotify Camp Nou, domin ganin yadda zata kaya.
Haka nan ƙungiyar ta kwashe sama da shekara guda ba tare da tayi rashin nasara a filin ba, domin rashin nasara ta ƙarshe da tayi a nan ita ce a hannun Villarreal a ranar 18 ga watan Mayun shekarar bara, gashi kuma tayi nasara a wasanni 6 cikin 7 na haɗuwarsu.
Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..............